Ziyarar aiki da Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai kasar Faransa bisa gayyatar shugaban kasar, Emmanuel Macron, ta sake bayyana wa duniya kyakkyawan kudirin kasar Sin na kyautata alaka da duk kasashen duniya domin daidaita al’amuran da samun ci gaba mai dorewa a tafarkin zaman lafiya ba tare da zubar da jinin ko da dan tsako ba.
Kowa ya san irin taratsi da hargitsin da kasashen yamma suka jefa duniya a ciki inda a yau kusan a kowace kusurwa ana samun tashe-tashen hankula ko dai da makami ko kuma da mukami. Amma kuma ziyarar ta Shugaba Xi a Faransa wacce ta zo a bana da Jamhuriyar al’ummar kasar Sin ke cika shekara 75 da kafuwa ta kara aike sakon cewa ana iya yin aiki tare don cimma kyawawan manufofi na ciyar da dan Adam gaba.
Daga mukalar da Shugaba Xi ya rubuta aka wallafa a fitacciyar jaridar nan ta Faransa, Le Figaro, ya jaddada kudirin kasar Sin na kara bude kofarta ga kasashen duniya da zurfafa hadin kai da Faransa har ma da sauran kasashe domin a gudu tare a tsira tare. Wannan a fili yana nuna wa duniya cewa kasar Sin ba ta rowar kaifin basira da hikimomin da ta yi amfani da su wajen zama kasa ta biyu mafi girman tattalin arziki tare da tsame daruruwan miliyoyin mutanen karkara daga kangin talauci. Kuma bisa bunkasar tattalin arzikin da ta samu a bara da kashi 5.2 da kuma hasashen samun na bana da kashi 5 cikin 100, Sin tana mika goron gayyata ga kowa da kowa ya zo ya ci gajiyar damarmakin da ke kasar, kasancewar kasar za ta ci gaba da zama turbar ciyar da duniya gaba.
Ba da wasa kasar Sin take zancen bude kofarta ba, misalin da Shugaba Xi ya bayar kan haka shi ne, “Muna maraba da karin kayayyakin amfanin gona da kayan kwalliya na kasar Faransa zuwa kasuwannin kasar Sin don biyan bukatun jama’ar kasar Sin da ke ci gaba da karuwa don samun ingantacciyar rayuwa. Muna maraba da saka hannun jari daga kamfanonin Faransa da na sauran kasashe a kasar Sin. Yanzu haka, mun bude kofar sashen masana’antun sarrafa kaya na kasar Sin gaba daya, kuma za mu hanzarta fadada hanyoyin shiga kasuwar sashen sadarwa, da likitanci da sauran ayyuka. Har ila yau, muna da wani shiri na dauke biza na kwanaki 15 ga baki daga kasashe da yawa ciki har da Faransa, kuma mun dauki karin matakai don saukaka tafiye-tafiye da biyan kudin baki a kasar Sin.”
Kasar Sin ba ta tsaya nan, tana ci gaba da karfafa gwiwar kamfanonin kasar su fadada ayyukansu zuwa kasashen duniya. A karkashin wannan, akwai kamfanonin kasar sama da 10,000 a Afirka da ke gudanar da aikace-aikace daban-daban musamman a karkashin kawancen Dandalin FOCAC.
Kasar Sin tana kara mara baya ga kamfanoninta su ci gaba da zuba jari a kasashen waje domin cin moriyar juna, a kan haka ne Shugaba Xi ya yi fatan Faransa za ta tabbatar da cewa kamfanonin Sin suna samun adalci wajen gudanar da kasuwancinsu daidai-wa-daida.
Wani abu mai muhimmanci da Shugaba Xi Jinping ya yi tsokaci a kai a mukalar tasa shi ne yadda kasar Sin za ta karfafa cudanya da hadin gwiwa da Faransa don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
A bana an cika shekaru 70 da kafa ka’idoji biyar na zaman tare cikin lumana. Shekaru 70 da suka wuce, tsohon firaministan kasar Sin marigayi Zhou Enlai ya gabatar da cikakkun ka’idojin guda biyar a karon farko, sun kunshi “mutunta mulkin kai da cikakkun yankunan kasa na juna, da rashin cin zarafi a tsakanin juna, da rashin tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan juna, da zaman daidaito da cin moriyar juna, da zaman tare cikin lumana”.
A tsawon wadannan shekaru, kasar Sin da magabatanta sun nuna muhimmancin rungumar zaman lafiya a duniya har ta kai ga ka’idojin nan guda biyar sun samu gagarumar karbuwa tare da aiki da su wajen tafiyar da dangantakar kasashen duniya a zamanance.
Saboda amannar da kasar Sin ta yi da zaman lafiya da mutunta juna, a sama da shekaru 70 da ta yi da kafuwa, ba ta taba takalar yaki ko mamaye ko da taku daya na yankin wata kasar waje ba. Kasar Sin ita ce kasa daya tilo a duniya da ta shigar da batun tsayawa tsayin daka kan hanyar bunkasa zaman lafiya a cikin kundin tsarin mulkinta, kana ita ce kadai daga cikin manyan kasashe masu makaman nukiliya da ta kuduri aniyar kin fara amfani da makaman nukiliya.
A aikace, kasar Sin ta kasance a sahun gaba wajen ganin an samar da dawwamammen zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. Ta nemi a kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza kuma ta sha nuna goyon baya a kan samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu a tsakanin Palasdinu da Isra’ila kamar yadda kudirin Majalisar Dinkin Duniya ya tanadar. Bugu da kari, Sin na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin Ukraine da Rasha ta hanyar lalama da kuma nunar wa kasashen duniya illolin da wadannan fitintinun suke haifarwa ga duniya.
A gaskiya, da za a yi cikakkiyar aiwatar da muhimman shawarwari guda uku da Shugaba Xi ya gabatar a ’yan shekarun nan a kan samar da wasu tsare-tsare na ci gaban duniya, da samar da tsaro da kuma wayewa daidai da zamanin da muke ciki wadda suka samu goyon baya da amincewar fiye da kasashe 100, tabbas za mu yi bankwana da bankwana da duk matsalolin da suka yi wa duniya kamun kazar kuku.