A ranar 8 ga watan nan ne aka kaddamar da dandalin tattaunawa kan dunkulewar tattalin arzikin mabambantan kasashe, da neman ci gaba mai dorewa na kamfanoni na shekarar 2024, a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka, a matsayin wani muhimmin bangare na jerin bukukuwan yayata tamburan kayayyaki kirar kasar Sin a majalisar karo na 5.
Kamfanonin Sin fiye da 20 sun tura wakilai zuwa wajen bikin, inda suka raba fasahohin kamfanoninsu, na daukaka ra’ayin neman ci gaba mai dorewa, tare da samun damar raya harkokin kamfanonin na kasar Sin.
- Firaministan Sin: A Samar Da Karin Alfanu Da Tsaro Mai Dorewa Ga Jama’a
- Motocin Sabbin Makamashi Kirar Kasar Sin Sun Mamaye Duniyar Motoci
Wadannan kamfanoni na Sin da suka halarci bikin sun shafi sana’o’i na kera motoci, da kimiyya da fasaha mai alaka da yanar gizo ko intanet, da sabbin makamashi, da aikin samar da kayayyaki masu inganci da dai sauransu.
A dai wajen bikin, Glenn Hodes, babban jami’i mai ba da shawara na MDD mai kula da aikin tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa tsakanin shiyyoyi, ya ce ana maraba da zuwan masu masana’antu na kasar Sin, don su raba fasahohi da labaru na tamburan kasar a MDD, kana ana fatan ganin shigar karin tamburan Sin cikin ofishin na MDD.
Ban da haka, masu masana’antu na kasar Sin sun sa hannu kan ‘Sanarwar tamburan kasar Sin a MDD”, inda suka yi alkawarin nuna gaskiya, da tsimin makamashi, da tabbatar da ci gaban al’amura masu dorewa, da sauke nauyin dake bisa wuyansu na raya al’umma, da gadon nagartattun al’adun kasar Sin, don daukaka matsayin tamburan kasar Sin a zukatun al’ummun kasashe daban daban. (Bello Wang)