Kwamishiniyar lafiya ta jihar Zamfara, Dr Aisha Anka ta tabbatar da bullar wata sabuwar cuta da ba a santa ba a jihar, wanda ya zuwa yanzu an samu mutuwar akalla mutum hudu, mutane 177 kuma sun kamu da cutar.
Jami’in yada labarai a ma’aikatar, Bello Ibrahim, ya bayyana haka a takardar da raba wa manema labarai.
- An Kori Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Zamfara Tukur Danfulani Daga Jamiyyar
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 30 Da Wani Malami A Zamfara
A cewar kwamishinan cutar na da nasaba da kumburin ciki da taruwar ruwa a ciki da kara girman hanta da sanya zazzabi da raunin jiki gaba daya.
An gano cutar a Kananan Hukumomin Maradun, Shinkafi da Gusau a jihar.
Yara cuta ta fi shafa, kuma ana tunanin samuwar cutar na da alaka da ruwan sha.
An kai rahoton lamarin ga Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC) da dukkan Hukumomin lafiya masu ruwa da tsaki a kan lamarin.
Yanzu haka ma’aikatar lafiya tana kan matakin bayar da agajin gaggawa don gano musabbabin bullar cutar a jihar.