Sojojin Janhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo sun daƙile wani yunƙurin juyin mulki a kusa da ofishin shugaban ƙasar Felix Tshisekedi da ke birnin Kinshasa a yau Lahadi.Lamarin ya faru ne da sanyin safiya kusa da gidan ministan tattalin arzikin ƙasar Vital Kamerhe da ke yankin Gombe, kusa da ofishin shugaban ƙasar da ke Palais de la Nation.
Janar Sylvain Ekenge da yake magana a gidan talabijin na ƙasar ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile yunƙurin juyin mulkin. Ya bayyana cewa duk masu haɗa baki don kawo tarnaƙi ba za su sake yin wata barazana mai tasiri ba.
- NDLEA Ta Cafke Mai Ciki Da Kudin Jabu Naira Miliyan 3.2
- Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 386 Bayan Garkuwa Da Su Shekara 10 A Dajin Sambisa
An bayar da rahoton jin ƙarar harbe-harbe a kusa da Palais de la Nation a lokacin yunƙurin juyin mulkin, a cewar majiyoyi da dama. Sai dai Janar Ekenge bai yi karin bayani kan abubuwan da suka faru ko kuma ainihin waɗanda ke da hannu a lamarin ba.
Kamfanin dillancin labaran na AFP ya yi ƙoƙarin tuntubar majiyoyin hukuma amma ba a samu wata amsa ba. Mutane 3 ne dai aka rawaito sun rasa ransa kawo yanzu kuma an kama wasu da dama ciki har da wasu ƴan ƙasar waje.
Da safiyar yau al’amura sun lafa a birnin Kinshasa, kamar yadda ƴan jaridar AFP suka ruwaito. Tun da farko dai rahotannin kafofin sada zumunta sun bayyana harin da cewa wasu mutane ne ɗauke da makamai suka kai gidan Kamerhe, inda wasu daga cikinsu suka koma Palais de la Nation.
Dama dai tuna masu sharhi suke tunanin zai yi wahala ba a kitsa wani juyin mulkin ba saboda ƙasashen turawa musamman Faransa bata goyon bayan juyin mulkin.