Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai kawo muku yadda za ku hada Yam Cake:
Abubuwa da uwargida za ta tanada:
kayan Miya (Dai-dai), Nama, sikari, magi, doya, gishiri, kori, tayim:
Yadda za ki hada:
Da farko za ki samu doyarki mai kyau guda daya ko fiye da haka ki fere ta ki yanka dai-dai misali ki zuba sikari babban cokali daya a ciki sai ki dora a wuta.
Sannan ki wanke naman ki sa tayim ki yanka albasa da magi guda daya ki sa ruwan daidai yadda zai dafa naman har ya tsotse, sai ki dora akan wuta har ya dahu. Idan ya dahu sai ki nika shi ko kuma ki daka shi da attaruhu kamar biyu tattasai daya ki goga albasa ki zuba akan naman bayan kin daka, kin sa magi ki juya ya hadu ki soya shi kamar danbun nama amma sama-sama kamar minti goma, sai ki yanka kwai wanda dama kin dafa shi kamar guda uku ko hudu akai.
Sannan ki koma kan doyarki da ta dahu kika sauke har ma ta fara shan iska, ki murmushe ta ko ki daka sama sama kar dai ta dahu sosai sai ki zuba magi da gishiri ki samu firayin fan wanda ba ya kamawa ki zuba mai kamar cokali biyu ko uku, sannan ki raba dakakkiyar doyar zuwa gida hudu naman ma ki raba zuwa gida uku, sai ki dauko doyar kashi daya ki zuba a cikin kaskon ki dauki naman kashi daya ki zuba saman doyar dama kuma kin kada kwanki a gefe, sai ki zuba ya lullube doyar da naman.
Daga nan sai ki sake zuba doyar a saman kwan ki sake zuba naman da kwan har kaskon ya kusa cika sai ki zuba kwan da yawa yadda dai lullube su gaba daya ki dora a wuta, amma fa kar ki bashi wuta sosai, ki bar shi kamar minti 20 zuwa 30 ki samu murfin tukunya wanda za ta rufe kaskon ki rufe yadda kwan sama zai dahu, shike nan an gama. Idan ya gama sai ki samu faranti mai kyau ki kwakkwafe a hankali za ki ga ya fita kamar cake sai ki sa wuka ki yanka yadda kike so, kuma kina iya gasawa a oben, a ci dadi lafiya.