Sojojin Nijeriya biyu sun rasa ransu a wani iftila’in da ya afku a garin Aba na jihar Abia a yau Alhamis lokacin da ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi wa wasu sojojin kwanton ɓauna a mahadar Obikabia da ke tsaunin Ogbor.
Harin ya zo daidai da ranar tunawa da mayakan Biafra (IPOB) wanda yan asalin yankin Kudu maso Gabas ne, a yanzu haramtacciyar kungiyar ce a bisa dokar Nijeriya.
- Dattawan Kudancin Kano 103 Sun Buƙaci Gwamna Abba Ya Dawo Da Sarakuna 5 Da Aka Rushe
- Sojojin Nijar Sun Cafke Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Zamfara
Hotunan faifan bidiyo da aka saki a shafukan sada zumunta sun nuna sakamakon harin kwantan ɓaunar da aka yi, ciki har da wata motar soji da aka kona da kuma harbe-harbe a kan titunan da babu kowa, lamarin da ke nuni da zaman ɗarɗar a yayin da mazauna yankin suka bi dokar zaman gida ma tilas ba bisa ka’ida ba.
Har yanzu dai ba a san ko su waye maharan ba, kuma rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba.
A baya dai kungiyar IPOB ta ayyana zaman gida a fadin jihohin Kudu maso Gabas domin karrama waɗanda aka kashe a yakin basasar Najeriya. Duk da cewa gwamnatin jihar Enugu ta yi watsi da wannan doka tare da kara ɗaukar matakan tsaro.