Shugaban jam’iyyar SDP, Hon Bala Muhammad Gwagwarwa ya bayyana cewa irin tafiyar siyasarsu akida daya suke da NEPU da PRP, wanda wannan akida na nufi yaki da talauci, lalaci, jahilci, zalunci da kuma ‘yantar da dan talaka ya zama ana damawa da shi a tsarin mulkin dimokuradiyya.
Ya ce akitar ta kasance ‘ya’yan talakawa su samu damar zama shugabani a kowanne mataki na mukamin mulkin Nijeriya, sakamakon gwagwarmaya da NEPU ta yi a sama da shekara 60 da suka wuce. Ya ce an kafa NEPU a ranar 8 ga watan Agusta ta shekarar 1958 da mutum 8 a Kano.
A cewarsa, shi jikan NEPU da PRP ne da aka kafa a 1978 ta Malam Aminu Kano, don haka ne ya ga ba zai iya tafiya da jam’iyyun PDP, NNPP, da APC ba, wannan ce ta sa ya koma jami’yyar SDP mai alamar doki domin ceto dimokuradiyya a Nijeriya.
Hon Bala Muhammad Gwagwarwa ya kasance tsohon shugaban karamar hukumar Nassarawa a jami’yyar SDP a shekarar 1990, ya ce dama wannan ce jami’yarsa kuma ita ya koma a yanzu kamar dai yadda ya bayyana a wani taron gangami na magoya bayansa da suka fice daga jami’yyar APC zuwa jamiyar SDP a Kano.