Wata mummunar guguwa da aka yi a daren ranar Asabar a cikin garin Bauchi ta janyo asarar rayukan mutum hudu a IBB Square inda ake gudanar da kasuwar baje kolin duniya ta arewa maso gabas.
Muhallin IBB square da ke Bauchi dai tsawon makonni ya karbi bakwancin kasuwar baje koli na shiyyar arewa maso gabas inda jihohin da ke shiyyar suka halarta. Guguwar ta yi barna a rumfunan jihar Gombe da Yobe, da kuma tantunan kasuwanci daban-daban da suke cikin kasuwar.
- Sanata Saliu Ya Raba Taki Da Injinan Ban Ruwa Ga Manoman Kwara
- Kwamishinan Bauchi Ya Rasu A Hatsarin Mota
A kokarin aikin ceto da ‘yansanda da sauran jami’ai suka yi, sun shiga tantuna da rumfuna domin lalubo wadanda tsautsayin ya rutsa da su inda suka kwashi wadanda suka gamu da barnar zuwa asibiti domin neman kulawar gaggawa na likita.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, kakakin rundunar ‘yansanda a jihar Bauchi, SP Ahmad Muhammad Wakil, ya ce, mutum biyar ne aka samu a cikin gine-ginen da suka rufta din, inda hudu daga cikinsu suka rasa rayukansu.
Wadanda suka rasa rayukansu din su ne Abdullahi Abubakar, dan shekara 38 da ke unguwar Yakubu Wanka, Sadiq Ahmed Alfa, mai shekara 32 mazaunin unguwar Fadaman Mada, Malam Musa daga Maliya Ventures, Tudun Salmanu da kuma Abdullahi Abdurrahman wanda ya fito daga jihar Gombe.
“Mace daya ce taf ta tsira daga cikin mutum 5 da hatsarin guguwar ta shafa wato Fatima Isa ‘yar shekara 31 da ta ke unguwar Inkil a cikin garin Bauchi, wacce a yanzu haka take amsar kulawar likitoci a asibiti.”
Hukumomi dai sun dukufa daukan matakan da suka dace ciki har da kai gawarwakin mamatan zuwa dakin adana gawarwaki da kuma bibiyar irin asarar da aka tafka sakamakon guguwar.
Tunin dai a cewar Wakil, ‘yansanda suka bazama wajen tabbatar da cewa bata-gari ba su yi amfani da wannan damar wajen yi wa ‘yan kasuwan baje kolin sata ba domin tabbatar da kare musu dukiya.