A ’yan kwanakin baya, ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin ya fitar da rahoton shekarar 2023, game da keta hakkokin bil Adama dake wakana a kasar Amurka, wanda ya fallasa yanayin kara tabarbarewar hakkin bil Adama a kasar, inda aka gabatar da shaidu da alkaluma kan hakan.
Rahoton ya nuna yadda Amurkawa ke shan fama da matsaloli masu nasaba da keta hakkinsu na ’yan kasa da na siyasa, inda ’yan siyasar kasar ke watsi da alkawuran da suka dauka na kare martabar alumma, maimakon haka, ba abun da ake gani illa nuna wariyar launin fata, da koma bayan tattalin arziki da rashin daidaito, da keta hakkokin mata da yara kanana da sauransu. A daya hannun kuma yadda kasar ke aiwatar da manufofin baba-kere, da shiga sharo ba shanu sun kara haifar da matsalolin jin kai da tashe-tashen hankula a sassa daban daban na duniya.
- Kasar Sin Na Hada Kai Da Kasa Da Kasa A Kokarin Inganta Muhallin Halittun Duniya
- Mafarkin Amurka Ya Rube Saboda Tsanantar Gibin Dake Tsakanin Matalauta Da Masu Arziki
Ko shakka babu lura da wadannan abubuwa na zahiri da Amurka ke fama da su, muna iya cewa kasar ta gaza wajen sauke nauyin alummunta na kare musu hakkokinsu.
Bisa alkaluman kididdiga, a kiyasin da aka yi a shekarar 2023 da ta gabata, adadin Amurkawa da aka hallaka ta hare-haren bindiga sun kai 43,000, adadin da ya kai kimanin mutum 117 ke nan a duk rana guda, baya ga a kalla mutane 1,247 da matakan amfani da karfin tuwo fiye da kima na ’yan sanda suka haifar da rasuwar su.
A bangaren tattalin arziki kuwa, gibin dake akwai tsakanin masu dukiya da matalauta a kasar ya kai matsayin koli a baya bayan nan, sama da yadda aka taba gani cikin shekaru masu tarin yawa.
Sai dai duk da wannan matsaloli, masu nasa da gaza kare hakkokin bil Adama da Amurkawa ke fuskanta a cikin gida, ’yan siyasar kasar da gwamnati na kawar da kai, tare da yunkurin bankado wasu zarge-zarge da suke dorawa sauran sassan kasa da kasa. Ga misali, a baya bayan nan, maaikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da rahoton nazarin hakkokin bil Adama na shekarar 2023, mai kunshe da wai hali da kasashe da yankuna kusan 200 ke ciki game da kare hakkin dan Adam, amma abun mamaki shi ne babu wani bayani cikin rahoton, wanda ya yi tsokaci kan halin da ita kanta Amurka ke ciki a wannan fanni.
Tabbas, wannan yanayi ya yi kama da karin maganar bahaushe da kan ce Laifi tudu ne ka taka naka ka hango na wani. A zahiri Amurka ta nuna halayyarta ta danniya, da nuna fin karfi, da son kai da munafurci.
Masharhanta da dama na ganin duniya ta riga ta farka, alummunta suna iya gane inda aka dosa, kuma jamaa suna kara gane masu kaunar zaman lafiya, da masu son tada zaune-tsaye, kamar dai yadda hakan ya bayyana a fili yayin rikicin kasar Israila da alummar Falasdinawa da har yanzu ya ki ci ya ki cinyewa. Duniya ta ga yadda kasashe da dama masu son zama lafiya ke ta kiraye-kiraye na dakatar da wuta, da kawo karshen yaki, yayin da Amurka a nata bangare ta gaza amfani da tasirin ta domin goyawa wannan manufa baya, alamarin da karara ke nuni ga goyon bayan da take yiwa manufar keta hakkokin biladama.
Wajaba Amurka ta yiwa kanta alkalanci, ta sauka daga matsayin mai yin baki biyu, kuma a maimakon mai nuna yatsa ga sauran sassa kan batun kare hakkin bil Adama, kamata ya yi ta sauke nauyin dake wuyanta na goyon bayan wanzar da zaman lafiya a cikin gidanta, da ma a fagen kasa da kasa.
Kaza lika, ya zama wajibi ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin sauran kasashe, ta kuma daina shiga harkokin sauran sassa dake bin nasu tsarin na kare hakkokin bil adama, kana ta sauka daga matsayin mai rura wutar yake da tashin hankali. (Saminu Alhassan)