Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa farashin shinkafa da gari da tumatur sun karu da kaso 141 a cikin shekara guda, shekarar ce da ta fi kowace shekara fuskantar karuwar farashin nasu, a cewar bayanan rahoton farashin kayan abinci.
Rahoton ya yi nuni da cewa farashin shinkafa ya karu da kaso156 zuwa Naira 1,399 a 2024, daga Naira 547 a shekarar 2023.Kazalika, farashin gari wanda shi ne mafi akasirin talakawa ke amfani da shi, ya karu da kaso135 daga Naira 363 a watan Afrilun 2023 zuwa Naira 852 a shekarar 2024, cikin shekara guda kacal.
- Matsalolin Tsaro Da Ambaliya: ‘Yan Nijeriya Sun Sayo Abinci Daga Waje Na Tiriliyan 3 – CBN
- NAHCON Ta Karyata Rahoton Bayar Da Abinci Mara Inganci Ga Alhazai A Makkah
A wata-wata, ya karu da kaso 13.59 daga Naira 750 a watan Maris zuwa Naira 1,554 a watanMaris. Rahoton farashin kayan abinci da suka hada da irin su albasa, shinkafa, wake, buredi,da nama, da tumatur da gari, ya karu sosai idan aka yi la’akari da farashinsa a watan Afrilu.
Farashin tumatur ya karu da kaso 17.9 daga Naira 960 a watan da ya gabata zuwa Naira 1,123 a watan Afrilu. An samu karuwar kaso 132 a cikin shekara-shekara daga Naira 485 a shekarar da ta wuce.
A cewar rahoton hukumar NBS, farashin gari mai nauyun 1kg ya karu da kaso 13.59 daga Naira 750 a Maris zuwa Naira 852a Afrilu an samu karuwar kaso135 a cikin shekara guda idan aka duba rahoton farashin a 2023.
Farashin wake ya karu da kaso 125 a shekara da ga Naira 616 na watan Afrilun 2023 zuwa Naira 1,388 a watan Afrilun 2024.