Matsalolin da ke addabar iilmi na da tarin yawa a Nijeriya, musamman idan aka yi la’akari da yadda aka watsi da shi tare da rashin ba shi muhimmancin da ya dace.
Ilimi wani muhimmin ginshiki ne da ke bayar da damar sanin abubuwan daban-daban, musamman na bangaren ci gaban al’umma baki-daya.
Duk da wannan muhimmanci da ilimi ke da shi, amma ana ci gaba da fuskantar matsaloli a makarantu da sauran wuraren koyar da ilimi a fadin wannan kasa.
Don haka, idan har aka kasa magance matasalolin da suke addabar ilimin, ko shakka babu zai ci gaba da tabarbare ne har zuwa illa masha Allahu.
- Gwamna Yusuf Zai Ayyana Dokar Ta-ɓaci A Fannin Ilimi A Kano
- Gudunmawa 10 Da Ilimi Ke Bayarwa Ga Al’umma (2)
Shahararren masanin nan a bangaren ilimi, Kolawole Yetunde; ya bayyana yadda wadannan matsaloli ke ci wa harkokin ilimi tuwo a kwarya a halin yanzu.
Yetunde ya ce, abu na farko shi ne rashin ware wa bangaren isassun kudade daga gwamnatocin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi.
A waannan shekara da muke ciki ta 2024, Nijeriya ta ware wa sashen ilimi kaso mafi karanci, wanda ko kadan bai kai kashi 26 cikin 100 na kasafin kudin da aka gabatar ba, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta nema.
Majalisar Dinkin Duniyar ta ba da shawara ne kan cewa, kowace kasa ta rika ware wa bangaren ilimi akalla kashi 26 cikin 100 na kasafin kudin kasar, don bunkasa harkokin da suka shafi ilimi.
Sai dai kuma wani abin takaici, tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a kasafin kudin da ya gabatarwa Majalisar Dattawa a shekakar 2018, kashi 7.04 kacal aka ware wa wannan bangare na ilimi, wanda gaba daya kasafin kudin shekarar Naira tiriliyan 8.6 ne.
Don haka, abin da aka ware wa sashen na ilimi; Naira biliyan 605, inda kuma za a yi amfani da Naira bilyan 435.1 wajen biyan albashi, alawus- alawus da kuma tafiye-tafiye. Haka nan, an ware Naira bilyan 61.73 a matsayin kudaden ayyuka da kuma Naira biliyan109.06 na hukumar kula da ilimin bai-daya.
Haka zalika, rashin iya tafiyar da aiki yadda ya dace da kuma cin hanci da rashawa daga bangaren masu zartarwa, su ne babban manyan dalilan da suka wannan bangare na ilimi ci gaba.
Kazalika, halin ko-in-kula da gwamnati ke nuna a kan harkokin da suka shafi bangaren, su ma suna taimakawa wajen ci gaba da tabarbarewar harkar a Nijeriya.
Bugu da kari, gwamnatocin, jihohi, tarayya da kuma kananan hukumomi, sun yi buris da abubuwan da suka shafi ilimi, domin kuwa ba sa ba shi irin muhimmancin da ya dace, wanda hakan ke matukar kawo wa bangaren koma-baya.
Haka nan, batun cin hanci da rashawa wanda ya riga ya zama ruwan dare a fadin wannan kasa, domin kuwa akwai labarun da ke nuna cewa; har manyan makarantunmu na jami’a, akwai malaman da ke karbar cin hanci daga wurin dalibai; su ba su sakamako mai kyau.
Sannan, masu makarantu na amsar kudi daga wurin dalibai, su aike da sakamakon jarabawarsu zuwa hukumar da ke kula da harkokin yi wa kasa hidima. Kazalika, masu neman a dauke su, don samun gurbin karatu a jami’oi, su ma na ba da kudi kafin a ba su wannan dama.
Wadannan matsaloli kusan haka suke a dukkanin sauran makarantun da suka hada da na fasaha, Kwalejojin ilimi, makarantun Sakandare da kuma na masu zaman kansu.
Rashin kula da ayyukan da aka dora wa jami’i daga bangarori daban-daban, ta fuskar kwarewar aiki; matsalar ba iya ta Nijeriya ce kadai ba, ta shafi kusan yawancin kasashen Afirkabaki-daya.
Har ila yau, har yanzu an kasa gane batun kula da ilimin firamare, yana karkashin kulawar gwamanatin tarayya ne ko jihohi ko kuma kananan hukumomi, wanda wannan ba karamar matsala ba ce; wajen samun ci gaban bangaren ilimin bai-daya.