Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata, inda yau kuma za mu yi magana kan yadda ake hadin nama da shinkafa cikin kwai.
Abubuwan da uwargida za ta tanada:
Shinkafa, Kwai, Nama, Peas, Karas, Albasa Daa Lawashi, Attaruhu Da Tattasai, Mai, Tafarnuwa, Magi, Gishiri Tayim da Kori:
Yadda uwargida za ta hada:
Ki samu markadadden namanki, ki zuba a tukunya. Ki samu Kori, Tafarnuwa, Lawashi, Tayim, Magi da Gishiri ki zuba ki juya sai ki barshi ya dahu. Sannan ki wanke shinkafa ki yi mata rabin dahuwa, sai ki kara wanke ta ki tsame ta da matsami, sai kuma ki dauko wannan naman ki zuba a kasko mai fadi ki zuba mai ki soya sama sama, sannan ki dakko shinkafarki ki zuba akai, sai ki sami Attaruhu ko Tattasai ki jajjaga ki zuba akai ki juya sai ki dakko Karas dinki da Peas ki goge bayan karas din ki yayyanka sai ki zuba ruwa ki juya sosai sai ki barshi zuwa ‘yan mintuna, sannan ki sami kwai ki fasa akai ki juya sosai sai ki barshi ya dan dahu sannan ki sauke, shikenan kin kammala.
Aci dadi lafiya.