Kawo yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers ta lashe kofin babbar gasar firimiyar Nijeriya a karo na takwas bayan doke kungiyar kwallon kafa ta Gombe United har gida da ci 2-1.
Rangers ta samu jimillar maki 70 a gasar ta Nijeriya Professional Footbal League (NPFL) kakar wasa ta 2023 zuwa 2024, wanda hakan ke nufin ta samu tikitin zuwa gasar Zakarun Afirka na shekara mai zuwa.
- Barazanar Da Rashin Katabus Na Kananan Hukumomi Ke Yi Ga Dimokuradiyyar Nijeriya
- Yadda Aka Yi Bikin Kaddamar Da Littafin Babban Editan LEADERSHIP A Abuja
An gudanar da bikin ba ta kofin ne a filin wasa na Jos International Stadium – inda Gombe United ke buga wasanninta na gida kuma bayan wasannin mako na 38 kamar yadda yake a doka.
Kungiyar Rangers ce ta fara cin kwallo minti uku da fara wasa ta hannun dan wasa Ogunleye, sannan Obaje ya kara minti hudu bayan haka, kafin Hassan ya farke wa Gombe kwallo daya a minti na 25.
Tun a ranar 16 ga watan Mayu Rangers ta hada maki 67 a saman teburi da ya ba ta zama gwarzuwar gasar bayan doke Bendel Insurance 2-0, sai dai kafin lashe gasar, Rangers ta ci wasanni 21 cikin 38 da ta buga, ta yi canjaras bakwai sannan ta yi rashin nasara sau 10.
Remo Stars ce ta kare a mataki na biyu da maki 65, sai kuma kungiyar Enyimba a mataki na uku da maki 63, wadanda suka samu gurbin shiga gasar zakarun Afirka ta badi.
Kamar yadda aka saba, kungiyoyi hudu na kasan teburi ne ke sauka daga babba zuwa karamar gasar ta firimiya wato Nijeriya National League (NNL). kungiyoyin su ne Sporting Lagos, Doma United, Heartland da kuma Gombe United.
Wasannin da aka buga a ranar Lahadi ne suka tabbatar da an kammala gasar kuma an buga jimillar wasanni 370, cikin kungiyoyi 20 da suka fafata tsawon kakar wasa daya kuma ita ce karo na 52 a tarihi.
Ga wasu abubuwa 10 da suka faru a gasar:
1. Dan wasan Enyimba, Bictor Mbaoma, shi ne kan gaba wajen jefa kwallaye a raga bayan ya ci kwallaye 16 a wasannin da ya fafata. 2. Dan wasan gaba na Kano Pillars, Yusuf Abdullahi, shi ne kadai ya ci kwallo sama da uku a wasa daya – inda ya ci Gombe United kwallo biyar a wasan da suka yi nasara 5-2 a kakar.
3 . ‘Yan wasa shida ne kacal suka ci kwallo uku rigis a wasa daya a kakar da aka kammala, su ne Robert Mizo (Bayelsa United), Yusuf Abdullahi (Kano Pillars) da dan wasa Albert Hillary (Plateau United), Nyima Nwagua (Ribers United), Silas Nenrot (Plateau United), Ubong Friday (Akwa United) da kuma Godwin Obaje (Plateau United).
4. Remo Stars ce ta fi kowacce kungiya karbar jan kati a kakar bana, inda aka bai wa ‘yan wasanta jan katin har sau bakwai – Enyimba ce ke biye mata da shida. 5 – Tun ana saura wasa daya a gama gasar Rangers ta dauki kofin wanda ba a fiya samun haka ba.
6. Doma United da ta sauka daga gasar, ta fi kowa buga wasa mai yawa ba tare da an zira mata kwallo a raga ba – da guda uku kawai ta dara zakarun gasar, wato kungiyar Rangers.
7 – Rangers sun fi kowa buga wasa mai yawa ba tare da rashin nasara ba, inda ta jera wasa 10 ba a doke ta ba – ta dara Doma United da wasa daya. 8 – Heartland wadda ta sauka daga gasar – ita ce ta fi kowa yawan wasa a jere ba tare da nasara ba. Ta buga wasa 11 babu nasara, sai kuma Doma da Gombe da suka buga 10-10 a jere babu nasara.
9 – Dan wasan Plateau United, Silas Nenrot, shi ne ya ci kwallo uku rigis a mafi kankantar lokaci a bana. Dan wasan gaban ya ci cikin minti 11 a wasan da suka doke Gombe United 4-0 a wasan mako 25.
10 – An ba da jan kati sau 49. 11 – An buga finareti 90, inda aka ci 70 kuma aka barar da 20.
12 – An ci kwallaye 848. 13 – Sau 29 kungiyoyoyi suka yi nasara a wasannin da suka buga a waje. 14 – Gombe ce ta fi kowa dibar kwallaye, inda aka zira mata 76 jimilla.
15 – An buga canjaras a wasa 86.