Biyo bayan rashin biyan albashi na wata tara daga gwamnatin Jihar Kaduna, ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha na jihar sun gudanar da zanga-zanga domin nuna damuwarsu kan yadda rayuwar ma’aikatan da take cikin wani muyacin hali bisa rashin samun hakkokinsu.
Zanga-zangar wanda Shugaban Kungiyar Ma’aikatan na Jihar Kaduna, Kwamared Umar Ladan, ya jagoranta ya bayyana damuwarsu matuka ganin yadda wasu da dama daga cikin ma’aikatan suke mutuwa bisa rashin samun hakkokinsu daga wurin gwamnati.
- ‘Yan Kasuwar Nijeriya Za Su Haɗa Hannu Da Gwamnatin Kaduna Wajen Bunƙasa Tattalin Arzikin Jihar
- El-Rufai Ya Maka Majalisar Kaduna A Kotu Kan Zargin Karkatar Da Biliyan 432
Ladan ya ce sun gudanar da zanga-zangar ne domin sanar da gwamnatin Jihar Kaduna halin da suke ciki na tsawon watanni tara babu albashi, inda suka bukaci Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da ya shigo cikin lamarinsu domin ceto rayuwarsu.
“Ya ce kwanan bayan mun rasa ma’aikatanmu guda uku saboda tasananin kuncin rayuwa. Daga daga cikin ya mutu ne lokacin da gwamnatin jihar ta biya mu kudin albashin wata daya. Yana samun sakon bankin cewa an biya albashi da ya je banki domin ya cire kudin sai suka ce babu kudi a cikin asusun ajiyarsa, saboda wai ya ci bashi a lokutan bayan kuma sun zare kudinsu.
“Wallahi nan take ya fadi ya mutu, saboda ya duba cewa idan ya koma gida ta yaya zai fuskanci iyalansa, wanda daman ga irin halin da ake ciki na tsadar rayuwa.
“Muna kira ga Mai Girma Gwamna Uba Sani da duba halin da ma’aikatan hukumar ruwa suke ciki ya kawo mana gudummawa domin ceto rayuwarmu da ta iyalanmu. Wata tara muka yi babu albashi,” in ji shi.