Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC a yankin arewa maso yamma, Salihu Lukman ya ce shugabannin siyasar arewa raunana ne kuma kawunansu rabe suke ba su da tsari.
A wata budaddiyar wasika da ya aike wa shugabannin a ranar Lahadi, Lukman ya ce ko shi kansa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ba ya kare muradin arewacin Nijeriya.
- Muna Jaddada Kiran A Tsame Masarautunmu Daga Rikicin Siyasa
- Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci
A cewarsa, yawancin shugabannin arewa sun damu da kare muradinsu ne kawai a cikin gwamnati.
“Babu shakka, shugabannin siyasar arewa suna kara rauni da rashin tsari. Hatta shi kansa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda shi ne babban mai rike da mukami a yankin arewa, ya kamata ya zama shugaban siysa a arewa.
“Tare da mutuntawa, zai yi wahala duk wani jami’in gwamnatin Asiwaju Tinubu daga arewa ciki har da Shettima ya yi kasada wajen kare muradun arewa.
“Abin takaici, yawancin shugabannin arewa sun fi damuwa da kare muradin kansu a cikin gwamnati.
“Saboda kariyar kai, tuni aka fara makircin zaben 2027. A cikin fadar shugaban kasa akwai alamun yakin, wanda ake zargin zai taso ne daga bangaren shugaban kasa.”
Lukman ya kara da cewa shugabannin arewa a jam’iyyun adawa su ma ba su dace ba, saboda sun fi mayar da hankali ne kawai wajen tsayawa takara a zaben 2027.
“Ya kamata mu ja kunnen shugabannin siyasa a kasar nan, saboda abubuwa na gab da kwace musu musamman a arewa.
“Idan ba a kula ba, yunwa da ta karade ko’ina a arewa zai iya sa mutane su fara shiga gidajen al’umma da wawashe dukiyoyinsu.
Lukman ya ce dole ne ‘yan Nijeriya su hada kai wajen samar da sabbin tsarin siyasa masu tasiri domin amfanin kasa.