Malam Yau Inuwa, jami’in Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ya mayar da wayoyi biyu da suka bata masu darajar Naira miliyan 4 ga mai su, Sheikh Muhajjadina Kano, a Filin Jirgin Saman King Abdulaziz dake Jeddah. Malam Yunusa Abdullahi, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ya sanar da wannan a cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Lahadi a Kaduna.
Abdullahi ya yaba wa Inuwa saboda gaskiyarsa, inda ya bayyana cewa ya mayar da wayoyin ne duk da suna da tsada, cikinsu akwai iPhone 5 da iPhone 15 Promax, yayin dawowar su Najeriya. Sheikh Kano ya nuna godiyarsa, inda ya bayyana cewa ya manta wayoyin a kujerarsa yayin da yake jiran a duba shi a filin jirgin. Ya shiga damuwa lokacin da ya gane cewa wayoyin, waɗanda ke ɗauke da muhimman takardu da bayanai, sun bata. Tsaron filin jirgin ya hana shi komawa domin dauko wayoyin har sai da Inuwa ya gano su kuma ya mayar masu.
- Matukin Jirgin Sojin Saman Nijeriya Ya Tsallake Rijiya Da Baya
- Nan Ba Da Jimawa Ba Makiyaya Za Su Ci Gaba Da Jigilar Dabobbi A Jirgin Kasa – NRC
Inuwa, wanda shi ne Jami’in Rijistar Alhazai na ƙaramar Hukumar Giwa kuma mai lura da dawo gida daga Jidda, ya kuma mayar da wasu jakunkuna guda bakwai na fasinjoji. Ya bayyana cewa ya lura da wasu mutane suna ƙorafin batan wayoyi a yankin duba fasinjoji, don haka ya yi azamar taimaka masu. Ayyukan Inuwa sun yi daidai da aikinsa na jami’in Hajj, inda ya tunatar da alhazzai su kula sosai da kayayyakinsu, musamman fasfo a filin jirgin.