ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (2)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
1 year ago
Allah

An farlanta wa Manzon Allah (SAW) yin Hajji a shekara ta shida bayan Hijira. Amma bai yi ba sai bayan Hijira da shekara 10.

Wasu malamai sun kawo hujjar cewa, bai yi Hajjin a shekara ta shida ba ne saboda a wannan shekarar Hajjin bai fado a cikin watan Zhul-Hajji ba. Haka nan a shekara ta bakwai, da ta takwas, da ta tara har sai a shekara ta 10 wanda a cikinta ne lokacin yin Hajjin ya zo daidai da watansa.

  • Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)
  • Manzon Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaba Nguema Na Gabon

A shekara ta tara, bayan ya nada Sayyidina Abubakar (RA) a matsayin Amirul Hajji a cikin watan Zhul-kida, sai ya sanar da duniya cewa badi zai je Hajji, duk mai son zuwa ya zo ya bi shi ya ga yadda zai yi (SAW).

ADVERTISEMENT

Malamai sun kara da cewa dalilin jinkirtawan har ila yau yana da alaka da al’adar da Larabawa suka kasance suna yi ta jujjuya Hajjin a watanni. Misali, idan a wannan shekarar an yi Hajji a watan Ramadan, badi sai su ce a watan Shawwal za a yi. A kan hakan, sai Annabi (SAW) ya jinkirta har zuwa shekara ta 10; lokacin da Hajjin ya fada a watan Zhul-hajji. Shi ya sa a ranar Arfa ya ce ya gode wa Allah duniya ta kewaya ta dawo wurin da aka halicce ta, dama Hajji a Zhul-hajji ake yi.

Imam Muslim ya ruwaito Hadisi wanda salsalarsa ke saduwa da Sayyidina Ja’afarus Sadik (RA) zuwa Babansa, Sayyidina Muhammadu Bakir (RA) cewa, “Mun shiga wurin Jabir bin Abdullahi, sai yake tambayar mutanen da muka shigo ko su wane ne; har dai ya zo kaina. Na ce ma sa ni ne Muhammadu Bakir dan Hussaini. Sai ya yi wawake ya dora hannunsa a kaina ya kama gashin kaina, ya kwance maballin rigata na sama sannan ya kwance na kasa, sai ya dora hannunsa a kirjina (don ya tuna irin kirjin Ma’aiki (SAW)), ni saurayi ne a wannan lokacin. Daga nan ya ce “lale da dan dan’uwana, tambayi abin da kake so. Na san kai malami ne, ilimi kake nema, so kake ka ji labarin kakanninka.

LABARAI MASU NASABA

Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed

MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi

Na zauna da Manzon Allah (SAW), na zauna da Sayyidina Aliyu, na zauna da Sayyidina Hassan da Hussaini, na zauna da Sayyidina Aliyu Zainul-Abidina (Babanka), don haka tambayi duk abin da kake so.” Shi (Jabir) makaho ne a lokacin, ina cikin tambayarsa kenan (in ji Ja’afarus Sadik) sai lokacin sallah ya yi, sai ya tashi a cikin wani dan mayafi da ya daura kuma ya yafa. Amma saboda kankancinsa duk lokacin da ya jefa shi a kafada sai ya fado alhali kuma ga babban mayafinsa a rataye a kantarsa. Sai ya yi mana sallah. Bayan gamawa na tambaye shi ya ba ni labarin Hajjin da Annabi (SAW) ya yi na karshe. Sai (Jabir) ya yi ishara da hannunsa tare da maganarsa, ya kure yatsunsa guda tara ya ce, “Annabi (SAW) ya zauna shekara tara bai yi Hajji ba, sannan ya yi izini a shekara ta 10 cewa zai yi Hajji a shekarar, sai mutane masu yawa suka taho Madina a shekarar ta 10, kowa yana so ya ga yadda Annabi (SAW) zai yi Hajji don ya yi koyi. Sai muka fita tare da shi (SAW) har muka zo Zul-hulaifa aka yi ta shirin harama.

Sai matar Sayyidina Abubakar Asma’u bintu Umaisin ta haifi dan da ya sa ma sa sunan Annabi (Muhammadu bin Abubakar). Ta aika (jaririn) zuwa wurin Annabi (SAW) kuma ta tambaye shi cewa ga shi ta haihu, yanzu ya za ta yi (da batun Hajjinta)? Annabi (SAW) ya aiko mata da amsar cewa, “Ke ma ki yi wankan harama da Hajji, daga nan ki yi kunzugu (Nafkin, wannan yana nuna macen da ba ta tsarki idan za ta yi Aikin Hajji dole sai ta yi wankan harama duk da cewa ba za ta yi sallah ko ta shiga Ka’aba ba). Sai Manzon Allah (SAW) ya yi sallah a Masallacin Zul-hulaifa, daga nan ya hau rakumarsa (Kaswa) har ta daidaita da shi a sarari. Sai na duba sarari; ga mahaya nan da masu tafiyar kasa a ko ina dama da hagunsa (SAW) iya ganina. Annabi (SAW) kuma yana tsakiyar yara (matasa), sai ya yi niyya ya daga muryarsa yana cewa “Labbaikal lahumma labbaik… zuwa karshe”, (ma’ana amsawarka ya Allah, ka ce in je Hajji kuma na amsa). Mutane su ma suka amsa. Mu dai (in ji Sayyidina Jabir), Hajji kadai (ban da Umura) muka yi niyya a lokacin, a haka muka rinka tafiya tare da Annabi (SAW) har muka zo Makka muka shiga Masallaci.

Farkon abin da Annabi ya fara yi bayan mun shigo Masallacin shi ne sumbantar Dutsen Hajarul As’wad. Sai ya fara Dawafi tare da sassarfa muma muna yi, har sai da aka yi zagaye uku sai (Annabi SAW) ya koma yin tafiya har aka yi zagaye hudu. Bayan haka, Annabi ya zo daidai Mukamu Annabi Ibrahim (AS) sai ya tsaya a bayansa, ya sa Mukamun a gabansa (tsakaninsa da Ka’aba), ya karanta ayar da ke cewa, “… Sai ku riki Mukamu Ibrahim a matsayin wurin Sallah”. Daga nan ya yi Sallar Nafila raka’a biyu, a ta farko ya karanta Kulya Ayyuhal Kafiruun, a ta biyu ya karanta Kulhuwallahu Ahad. Sai Annabi (SAW) ya koma ya sake sumbantar Hajarul As’wad. Daga nan ya fita zuwa kofar Safa, yayin da ya hau kan Safa sai ya karanta ayar da ke cewa, “Hakika Safa da Marwa alamomi ne daga alamomin Addinin Allah…” ya ce “Na fara da wanda Allah ya fara ambata”, da ya hango Ka’aba sai ya ce “La’ilaha illallahu wahdahu la shariykalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli sha’in kadiyr. La’ilaha illallahu anjaza wa’adahu…” Sannan ya yi addu’a (idan Alhaji ya haddace wannan ya karanta, idan bai haddace ba ya karanta Subhanallahi wal-Hamdulillah wal-Lahu akbar ko ya yi ta fadin la’ilaha illallah). Bayan Annabi (SAW) ya gama addu’ar sai ya sake maimaita wannan addu’ar sau uku, sai ya sauko daga Safa ya taho Marwa.

A lokacin da ya zo kwari (tsakiyar Safa da Marwa), sai ya yi sassarfa (a nan maza ke yin sassarfa, ban da mata). Da ya hau kan Marwa sai ya tsaya ya yi addu’a kamar yadda ya yi a Safa. Haka ya rika yi har ya kammala Sa’ayin a Marwa. Sai Annabi (SAW) ya ce “Idan na sa gaba kan abu ba na dawowa, da ban zo da abin hadaya ba, sai in yi Hajjin Tamattu’i in mayar da wannan Hajjin Umura. Amma yanzu duk wanda bai zo da abin hadaya ba, ya mayar da wannan Hajjin ya zama Umura (ya kwance haramarsa, ya yi aski)”. Sahabbai suka ce “Ya Rasulallahi bai fi kwana hudu a yi Arfa ba”, Annabi (SAW) ya ce “Ku cire haramar kawai, ku yi aski.”

Ba shikenan darasin ba, za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allah har da kawo darussan da hadisin yake nuna mana.

Allah
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Komawa Ga Allah Ta Hanyar Yawaita Istigfari
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Kula Da Tarihi A Musulunci
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Albishir Ga Iyayen Da Suka Karantar Da ‘Ya’yansu Alkur’ani (2)

MASU ALAKA

Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed
Siyasa

Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed

May 5, 2026
MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi
Addini

MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi

May 2, 2026
Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
Addini

Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…

March 20, 2026
Next Post
Ƴansanda Sun Kama Ƴan Daba 33 A Kano

An Kama Mutane 49 Da Ake Zargi Da Damfara A Jihar Kogi

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.