Kotun babban birnin tarayya (FCT) ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, na neman izinin tafiya Birtaniya domin neman magani. Hukumar yaƙi da Yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da Emefiele ne bisa zargin cin amanar ƙasa, yin jabun takardun kuɗi, haɗa baki, da samun kuɗi ta hanyar ƙarya yayin da yake matsayin gwamnan CBN.
Ɗaya daga cikin zarge-zargen shi ne cewa Emefiele ya buga jabun takarda daga Sakatare zuwa gwamnatin tarayya kuma ya ba wa kamfanoni biyu, April 1616 Nigeria Ltd da Architekon Nigeria Ltd, wanda haka ya ba shi damar tafka rashin adalci.
- Shugaban Bankin Duniya Ya Yi Tsokaci Kan Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin
- Ba Zan Taba Mantawa Da Zamowata Gwarzuwar Banki Sau Biyu A Jere Ba – Fatima Gana
Alƙalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu, ya yi watsi da buƙatar tafiyar Emefiele saboda ba a gabatar da wata takardar shaidar ganawar likita ko gayyata da za ta tabbatar da buƙatar tafiyar ba. Alƙalin ya jaddada cewa Emefiele na fuskantar tuhume-tuhume daban-daban a kotuna uku kuma babu isasshiyar hujjar da za ta sa a amince da buƙatar.
Lauyan Emefiele, Labi Lawal, ya nemi kotun ta saki fasfon Emefiele da aka ajiye a matsayin sharadin beli domin ya samu damar tafiya neman magani. Sai dai masu gabatar da ƙara sun yi adawa da buƙatar, suna cewa babu rahoton likita da ke nuna rashin lafiyar da ba za a iya magancewa a Nijeriya ba, kuma sun nuna damuwa kan yiwuwar guduwar Emefiele saboda alaƙar shi da ƙasashen waje.
Kotun ta yanke hukunci cewa hujjojin da lauyoyin Emefiele suka gabatar ba su da inganci don amincewa da buƙatar, don haka an yi watsi da ita.