A jiya ne kasar Sin ta fitar da alkaluman tattalin arzikinta na rabin farko na shekarar bana, inda yawan GDPn kasar ya zarce yuan triliyan 61, adadin da ya karu da kashi 5 cikin dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. Lallai, yadda kasar Sin ke kokarin neman sauye-sauye, yana ta samar da babban karfi ga tattalin arzikinta.
A wannan rana kuma, kasar Sin ta kara tashoshin kwastam 37 da ke iya kula da bakin da suke yada zango a kasar cikin sa’o’i 144 ba tare da samun biza ba, a yayin da batun “China Travel” ke matukar samun karbuwa daga wajen baki, wanda hakan ya zama karin matakin da ke samar da sauki ga baki da ke zuwa nan kasar Sin, haka kuma karin mataki ne da kasar Sin ta dauka na kara bude kofarta ga ketare, wanda tabbas zai jawo karin baki zuwa nan kasar don more damammakinta.
- Kasuwar Hayakin Carbon Ta Kasar Sin Tana Da Karko
- Amurka: Sarkin Leken Asiri Na Neman Habaka Karfinta
A hakika, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare a shekarar 1978, kasar ta samu gaggaruman nasarori wajen bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma, kuma alkaluman tattalin arzikin da aka samar, da bunkasar harkokin “China Travel” da ke matukar samun karbuwa, duka sun shaida hakan. Al’amuran da suka wakana sun yi ta shaida cewa, manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, muhimman matakai ne da kasar Sin ta dauka na zamanintar da kanta.
A kuma jiya ne aka kaddamar da cikakken zama na uku na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ko (JKS) karo na 20, taron da ya jawo hankalin kasa da kasa, amma me ya sa hakan?
A kan gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a shekaru biyar-biyar, kuma a tsakanin duk tarukan wakilan biyu, kwamitin kolin JKS ya kan kira cikakken zamansa har sau bakwai. A rahoton da kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya bayar, ya ce daga cikin tarukan da JKS take gudanarwa a kai a kai, cikakken zama karo na uku na da matukar muhimmanci, sakamakon irin tasirin da ya kan haifar ga kasar da ta zama ta biyu a duniya wajen karfin tattalin arziki. Har ila yau kuma a cewar kafar BBC, cikakken zama da kwamitin kolin JKS ya gudanar a karo na uku yana da ma’anar musamman a tarihin jam’iyyar. Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare, cikakken zama karo na uku da kowane kwamitin kolin JKS ya gudanar ya kan mai da hankali a kan yin gyare-gyaren tattalin arziki, wanda kuma ke taka muhimmiyar rawa ga bunkasuwar kasar Sin. Ana kuma sa ran tsara manyan manufofin da suka shafi gyare-gyaren tattalin arziki a wajen taron.
Lallai haka abun yake. Kasar Sin ta dauki manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare ne a gun cikakken zama karo na uku na kwamitin kolin JKS karo na 11 da aka gudanar a shekarar 1978, kuma tun daga lokacin, batun gyare-gyare ya zama babban jigo ga cikakken zama na uku da kowane kwamitin kolin JKS ya kira. Manufar yin gyare-gyare a cikin gida, da bude kofa ga kasashen ketare, ta samar da manyan sauye-sauye ga kasar Sin, haka kuma ta haifar da babban tasiri ga duniya. A gun zaman taron da ake yi a wannan karo, za a tsara ayyukan da za a yi wajen zurfafa gyare-gyare daga dukkan fannoni a kokarin da ake yi na zamanintar da kasar Sin, matakin da zai samar da alkiblar ci gaban kasar a gaba, tare da samar da karin damammaki ga kasashen duniya da ke fuskantar kalubaloli iri daban daban.
Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, kasar ta zamanto kasa ta biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, kuma karfin kasar da ma tasirinta a duniya sun karu kwarai da gaske. A yayin da wasu kasashe suke yunkurin rufe kofarsu ga sauran kasashen duniya, zaman taron da JKS ke yi ya shaida wa duniya cewa, kasar Sin za ta nace ga bin hanyar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, don kara amfanar da al’ummar kasashen duniya. Daidai da kalaman Hassan Ragab, shehun malami a jami’ar SCU ta kasar Masar, wanda ya ce taron da ake yi zai shaida niyyar kasar Sin ta zurfafa gyare-gyare daga dukkan fannoni, da ma zamanintar da kanta, kuma bisa tsarin hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”, zai sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
A sa’i daya kuma, bisa ga nasarorin da kasar Sin ta cimma, yanzu haka kasashen duniya sun san cewa ba hanya daya kacal ake iya bi wajen zamanintar da kai ba, kuma taron da ake yi zai kara shaida wa duniya hanyoyin da kasar Sin za ta bi wajen zamanintar da kanta, wanda hakan ke da matukar ma’ana ga kasashe masu tasowa har ma da duniya baki daya.
Kasar Sin na kan hanyar zuwa inda ta yi niyya, kuma tana samar da kwarin gwiwa da damammaki ga duniya, kuma za ta dada samar da kuzari ga duniya bisa ga yadda take yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen duniya.