Shugaba Bola Tinubu, ya bukaci Majalisar Dattawa ta yi gyara a kan dokar kasafin kudin bana da ta harkokin kudade ta bara ta hanyar kara Naira tiriliyan 6.2 a cikin kasafin kudin na bana.
A cikin wasikar da ya aike, shugaban ya bayyana cewar matakin ya dace da sashe na 58, karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka yiwa kwaskwarima.
- Kotu Ta Dawo Da Shaibu A Matsayin Mataimakin Gwamnan Edo
- Gwamnatin Kebbi Ta Ƙaddamar Rabon Taki Ga Manoma 48,000 Kyauta
“A nan ina gabatar wa majalisar dattawa da wannan kudiri domin ta yi nazari tare da zartar da shi.
“Kudirin dokar kashe kudade ta bana ya nemi a yi gyara a kan ainihin dokar da nufin samar da Naira tiriliyan 3 da bilyan 200 domin aiwatar da ayyukan raya kasa karkashin shirin “renewed hope” tare da sauran muhimman ayyukan raya kasar da ke gudana a fadin kasar nan.”
“Sannan naira tiriliyan 3 domin samar da karin kudaden da za a kashe yau da kullum, wadanda wajibi ne domin gudanar da harkokin kashe kudaden gwamnatin tarayya yadda ya dace, kuma ake sa ran samun daga asusun kudin shiga na gwamnatin tarayya.”
Tinubu ya kara da cewa ana bukatar yin kwaskwarima a kan dokar harkokin kudi ta 2023 ne, domin cazar haraji daga irin ribar da bankunan suka samu a hada-hadar musayar kudade kamar yadda bayanan hada-hadar kudadensu ta bara suka nuna.
Tinubu ya ci gaba da cewar an yi haka ne domin samun kudaden gudanar da ayyukan raya kasa da bunkasa ilimi da kiwon lafiya da tsare-tsaren sanya walwala a zukatan al’umma.