An kusa bude gasar Olympics ta Paris. Shugaban IOC Tomas Bach ya gode wa CMG bisa kyakkyawar shirin da ya yi don watsa shirye-shiryen wannan gasar Olympics.
Shugaba Bach ya ce gasar Olympics ta Paris ta shirya tsaf. Kuma CMG ya taka muhimmiyar rawa game da hakan, musamman a fannin amfani da gagarumin fasaha na 8K da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, wanda ya bude wani sabon mataki na watsa shirye-shiryen gasar Olympics. (Mai fassara: Yahaya)