Rundunar Ƴansanda ta Kano ta fara bincike gida-gida domin gano kayan da aka sace yayin zanga-zangar matsin rayuwa wato #EndBadGovernance. A farkon zanga-zangar an yi ta cikin lumana, amma daga bisani wasu Ƴandaba suka kwace ta, suka wawashe shaguna, da gidaje da cibiyoyin gwamnati, ciki har da ofishin Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) da ba a riga an ƙaddamar ba. Masu lalata dukiyoyin jama’a sun kuma lalata fitilun tituna da wasu kayan jama’a.
Ƴansanda sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka kama fiye da mutane 400 da ake zargi da hannu a rikicin, kuma sun gano wasu daga cikin kayan da aka sace.
- Zanga-zanga: Tattalin Arzikin Nijeriya Zai Yi Asarar Naira Biliyan 400 A Kullum -Masana
- Zanga-zanga: Kada Ku Mayar Da Kano Da Arewa Baya – Sanusi II
Sa’adatu Baba Ahmad, wata mai amfani da kafafen sada zumunta, ta bayyana cewa Ƴansanda sun fara gano kayan da aka sace daga yankin Yakasai da Durumin Zungura a Kano Municipal.
‘Yansandan sun sake jaddada ƙudirinsu na gurfanar da waɗanda suka aikata laifin gaban ƙuliya da kuma dawo da zaman lafiya a wuraren da abin ya shafa.