Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, ya ce shugaba Bola Tinubu yana bibiyar zanga-zangar #EndBadGovernance da ke wakana a duk fadin kasar.
Zanga-zangar na zuwa ne sakamakon tsadar rayuwa, sakamakon karyewar darajar Naira da kuma cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi.
- Rana Ta 3: Duk Da Dokar Hana Fita Masu Zanga-zanga Sun Fito A Kano
- Me Ya Sa Budurwa Take Juya Wa Saurayi Baya Farad Daya?
Ko da yake an yi kira ga Tinubu ya yi jawabi ga al’ummar kasar bayan zanga-zangar ta shiga rana ta uku – duk da cewa – har yanzu shugaban bai ce uffan ba.
Sai dai Bagudu, ya ce shugaban na Nijeriya ya san halin da ake ciki.
“Shugaban kasa yana bibiyar lamarin yadda ya kamata, “in ji ministan a ranar Asabar yayin shirin na musamman da gidan talabijin na Channels.
‘Ni minista ne. Ina kuma da nauyi. Na kuma sa ido kan wannan abu. Na dade ina lura da wannan abu domin na yi bayani.”
“Mun kasance muna sanya ido da kuma sauraro a hankali don jin abin da ake fada da abin da ke faruwa,” in ji Bagudu a cikin shirin.
Ministan ya gamsu cewar ‘yan Nijeriya na fuskantar wahalhalu, amma ya ce gwamnatin tarayya na kokarin ganin an samu saukin rayuwa ga ‘yan kasar.
“Kuncin rayuwa lamari ne da ya shafi kasashe da dama,” in ji shi.
Amma ya ce gwamnati na daukar matakan da suka dace domin saukaka wa ‘yan kasar.