Kungiyar kwadago (NLC), ta ce gungun jami’an tsaro dauke da tarin makamai sun yi wa hedikwatarta da ke Abuja, dirar mikiya.
Kungiyar ta ce jami’an sun isa ginin hedikwatar ne da ake kira Labour House, tun da daddare da misalin karfe 8:30
- Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Karshen Matsin Rayuwa – Gwamnan Bauchi
- Ma’aikatan NNPC Ba Barayi Ba Ne – Mele Kyari
A sanarwar da shugaban sashen hulda da jama’a na kungiyar, Benson Upah, ya fitar ya ce jami’an sun karya kofar dakin ma’ajiyar littattafai da ke hawa na biyu na ginin, inda suke debe daruruwan littattafai da wasu takardu
Sanarwar ta ce, jami’an sun yi ikirarin cewa suna neman wasu takardu ne da aka yi amfani da su a zanga-zangar matsin rayuwa.
Kungiyar wadda ta ce zuwa yanzu ba ta iya tantance abubuwan da jami’an tsaron suka kwashe ba, ta nemi da a gaggauta janye jami’an daga hedikwatar.
NLC ta bayyana yau a matsayin wata bakar rana a dimokuraduyyar Nijeriya, inda ta ce ko da a lokacin bakin mulkin sojoji ba a taba yi wa hedikwatarta abin da aka yi mata a wannan lokacin ba na kutse.
Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta yi zargin akwai wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar matsin rayuwa.