Hukumar shirya jarabawa manyan makarantu ta kasa (JAMB) ta fasa kwai a kan abinda ta kira “yadda ake jabun lamarin da ya shafi canza shekarun haihuwa ”a kan nambar takardar dan kasa da aka sani NIN wadda ake turawa hukumar domin a canza shekarun da aka sa.
Hukumar irin wannan halin yana da hadari, cutarwa abinda kuma ba dole bane, inda take cewa sai mai bukatar ya samu gurbin karatu ya kai a kalla shekara 16, a lokacin zai cancanci a dauke shi.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar JAMB, Dakta Fabian Benjamin, shi ne ya bayyana hakan wajen taron manema labarai ranar Lahadi ta makon da ya gabata a Abuja inda ya ce “Sai wadanda basu kai shekara 16 ba, ba za su samu damar a basu gurbin karatu ba, idan aka yi la’akari da matakin da aka dauka a taron tsarin hukumar na shekarar 2024.”
Duk da yake dai hukumar ta ba dukkan makarantu wa’adin wata daya domin su bayyana duk damar karatun da suka bada wadda ta wuce ka’idarta ta ta tsarin bada guraben karatu wato (CAPS) kafin shekara 2017.
Ya ce “Hukumar ta lura da yadda wasu makarantu suke bada damar guraben karatu ba tare da bin ka’idar ta ba, inda maimakon haka sai suka bi ta gurguwar hanyar su domin aikata abinda bai dace ba.”
“Saboda kawo karshen lamarin ya sa hukumar ta yanke shawarar jan layi saboda a daina aikata laifin da bai dace ba, inda ya kara jan hankali inda ya ce dukkan daliban da aka basu gurbin karatu kafin shekarar 2017.Wadanda bayanansu ke tare da shi wa’adin wata daya daga ranar 1 ga Augusta zuwa 31,2024; duk wani gurbin da aka bayar kafin 2017 ba za a amince da shi ba, idan har ba a bayyana hakan ba cikin wata dayan.”
Ya ce an ja kunnen makarantu su yi amfani da umarnin da aka basu, domin kuwa ba za a kara wani wa’adi ba, ba za a sake amincewa da wasu ‘yan makarantar da ba a shigar da bayanansu ba, wadanda ko ma rajista ba su yi da hukumar ba, ba ma a maganar sun rubuta jarabawarta ba’’.
‘’Wannan matakin an dauke shi ne domin ayi maganin yadda ake bada guraben ilimi ba tare da bin ka’ida ba da kuma sa bayanan karya, yayin da da za a rika tabbatar da ana bin dokar CAPS.”
Hakanan hukumar ta nuna rashin jin dadin ta akan abinda ake kira da suna yadda ake bada damar gurbin karatu wato wanda ake yi ko wace rana da wadansu makarantun fasaha da wasu ke yi da hadin bakin wasu Jami’o’i.
Benjamin ya ce “yana da kyau mutane su gane su wadancan nau’oin karatun hukumomin kula da ilimin fasaha da Jami’oi, basu amince da su ba.Dukkansu shigar kutse suke neman su yi ma tsarin ilimin Nijeriya.”
” Wata damfara ce da ake mantawa da masu nagarta kamar yadda tsarin dokar bada guraben karatu ta tanada ga wadanda za su kasance masu zama makaranta,a bi hanyar da bata dace ba wajen amfani da abubuwan da ba kan ka’ida suke ba, domin a samu kudaden da kan ka’ida suke ba. Ta haka sai a bata ma wadanda suke son shiga ta sahiyar hanya, tare da wadanda suke fandararru.
Daliban da basu yi kokarin azo a gani ba ko makin da bai taka kara ya karya ba, lokacin da suka yi jarabawar shiga manyan makarantu, irinsu ne ake jan hankalinsu, su je su yi irin karatun da ko sun kammala zai iya zame masu alakakai.
Ya ce an gano wasu makarantu da suke daukar dalibai da yawa ta hanyar tasarin karatun da ba a amince da shi ba, inda daga karshe su kan hada su tare da wadanda suka zauna a makarantar suke, amma sai su yaye su tare.