Ganin yadda kasar Sin ke da huldar kut da kut tare da kasashen Afirka, ya kan sa wasu ‘yan siyasa na kasashen yamma damuwa. Misali, a kwanan baya, mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Kurt Campbell, ya yi wani jawabi a gaban ‘yan majalisun dokokin kasarsa, inda ya ce ya kamata kasar Amurka ta kara kokarin takara da kasar Sin, saboda tasirin kasar kan kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka yana baya sosai, idan an kwatanta da na kasar Sin, abin da zai haddasa matsala ga kasar Amurka a kokarinta na neman samun wasu ma’adinai masu muhimmanci.
Ba shakka, a idon Mista Campbell, nahiyar Afirka wani fili ne da aka kebe wa manyan kasashe domin su gudanar da takara a tsakaninsu, da kwace albarkatun kasa, kana kasar Sin tana takara da kasar Amurka ne a cikin wannan fili. Sai dai ko maganar Campbell gaskiya ce?
- Kasar Sin Ta Samu Gagarumar Nasara A Wasannin Olympics Na Paris
- Kungiyar Kasar Sin Ta Lashe Lambar Zinare A Gasar Kwallon Tebur Ta Kungiyoyin Mata A Gasar Olympics Ta Paris
Hakika zancen Kurt Campbell, ya tunatar da ni da wani bayanin da masaniyar ilimin tattalin arziki ‘yar kasar Italiya Linda Calabrese, ta rubuta, mai taken “Sin da Afirka: Ko kasashen yamma za su iya koyon wasu abubuwa?”, wadda aka watsa shi ta shafin yanar gizo na jami’ar King’s College London ta kasar Birtaniya. Cikin bayanin na ta Linda Calabrese, ta ce ko da yake wasu kasashen dake yammacin duniya ba su son ganin mu’ammalar da ake yi tsakanin bangarorin Afirka da Sin, duk da haka, mutanen Afirka suna da yakini kan mu’ammalar. Inda a ganinsu, kasar Sin abokiyar hulda ce mai muhimmanci, kana kasar za ta dinga kawowa nahiyar Afirka damammaki na ciniki, da zuba jari, gami da samun ci gaban tattalin arziki.
To ko me ya sa kasar Sin ke samun karbuwa a nahiyar Afirka? A cewar Madam Calabrese, dalili shi ne ra’ayin kasar Sin kan kasashen Afirka ya sha bamban da na kasashen yamma. Da farko, kasar Sin tana kallon kanta a matsayin abokiyar kasashen Afirka, wadda ke hadin gwiwa da su bisa matsayin daidaito, maimakon wani bangaren samar da tallafi, wanda ya fi sauran kasashe ikon fada-a-ji. Na biyu shi ne, kasar Sin na ta kokarin zuba karin jari a kasashen Afirka, ba kamar yadda abun yake a kasashen yamma ba, inda kamfanoni kalilan na su ke zuba jari a nahiyar Afirka, kana kudin masu samar da tallafi na kasashen yamma shi ma ya ragu matuka.
Dalili na uku kuma shi ne kasar Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin gida na kasashen Afirka, kana tallafin da take ba su ba ya tare da wani sharadi, lamarin da ya janyo amincewa da yabo daga dimbin kasashen dake nahiyar Afirka, wadanda suka dade ba su samu kulawa daga kasashen yamma ba.
Sa’an nan wadanne matakai ne su kasashen yamma suka dauka don tinkarar tasirin kasar Sin a nahiyar Afirka?
A ganin Madam Calabrese, kasashen yamma sun dauki mataki mafi muni, inda maimakon dora isashen muhimmanci kan karfafa huldar hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, sun fi mai da cikakken hankali kan takara da kasar Sin. Calabrese ta ambaci wasu misalai: Rukunin G7 ya tsara wasu shirye-shiryen tallafawa kokarin gina kayayyakin more rayuwa a duniya, bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Tamkar an tsara shirye-shiryen ne musamman ma domin takara da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, a maimakon lura da yanayin koma bayan kayayyakin more rayuwa da kasashen Afirka suke ciki. Kana a nata bangare, kasar Amurka ta samar da shirin raya fasahohin dijital a Afirka, don neman maye gurbin kamfanonin Sin masu samar da hidimomin fasahohi na dijital, a kasuwannin Afirka, maimakon neman samar da dabara mafi dacewa ta cike gibin da ke akwai a kasashen Afirka a fannin fasahohin dijital.
Madam Calabrese ta kuma bayyana kurakuran kasashen yamma bisa yunkurinsu na takara da kasar Sin a nahiyar Afirka, wato da farko, ba su lura da hazakar mutanen kasashen Afirka da ta gwamnatocinsu ba. Hakika, dimbin nazarin da aka yi sun nuna cewa, kasashen Afirka suna iya daidaita huldarsu da sauran bangarori daban daban, gami da tabbatar da moriyarsu a mu’ammalar da suke yi tare da kasar Sin, da kasashen yamma, da sauran abokan hulda daban daban. Na biyu shi ne, kasashen yamma suna kallon nahiyar Afirka a matsayin wani abu mallakin su, wanda kasar Sin ke neman kwacewa. To amma wannan ra’ayi, a ganin Madam Calabrese, tamkar rashin masaniya da girmama tarihi ne, musamman ma ga kasashen da suka taba gudanar da mulkin mallaka a nahiyar Afirka.
A karshen makalarta, Linda Calabrese ta shawarci kasashen yamma, da su kulla huldar abota ta gaske tare da kasashen Afirka, da amincewa da mutunta moriyar bai daya da ake samu cikin huldar, maimakon mai da nahiyar Afirka wani fili na gudanar da takara tsakanin manyan kasashe.
A ganina, wannan shawara tana da ma’ana, domin kuwa ta nuna sanin ya kamata, kana ta zama daya da manufar kasar Sin ta hulda da kasashen Afirka. Amma abun tambaya a nan shi ne shin Kurt Campbell, da sauran ‘yan siyasar kasashen yamma masu ra’ayi irin na sa za su saurara?
(Bello Wang)