Matatar man Dangote ta yi watsi da rahotannin da wasu ke yadawa cewa ta kayyade farashin man fetur a kan ₦600 kan kowace lita.
Ta bayyana labarin a matsayin labarin karya muma mara tushe.
- NIS Ta Ƙaddamar da Sabon Tsarin Tsaurara Tsaro A Iyakokin Arewa Maso Gabas
- Gwamnati Ta Fara Tattaunawa Da ‘Yan Kasuwa Don Karya Farashin Kayan Abinci A Nijeriya
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban jami’in kula da harkokin kasuwanci na kamfanin Dangote, Anthony Chiejina ya sanya wa hannu a ranar Talata.
Wannan ya biyo bayan rahotannin da wasu jaridu suka yi cewa matatar tana tattaunawa da ‘yan kasuwar mai kan sayar da mai a kan farashin Naira ₦600 kan kowace lita.
Sai dai kamfanin ya jaddada cewa ba shi alaka da kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN).
Ya ce, “An jawo hankalinmu game da labarin da Jaridar Punch ta buga a ranar Talata, 13 ga watan Agusta, 2024.
“Muna so mu fayyace cewa kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya (IPMAN), ba mu kulla alakar kasuwanci da ita ba.”
Ya ci gaba da cewa, “Ba mu taba tattaunawa da su kan farashin man fetur ba, kuma ba su da hurumi.
“Muna kira ga jama’a da su nesanta kansu daga irin wannan hasashe. Muna da kafafen da muke sanar da masu ruwa da tsakinmu duk wani abu da ya shafe mu.”