Kalmar sangarta tana nufin duk wani abinda da ko ‘ya suka yi wanda bai dace ba, ba za a yi masu fada ba domin gudun kada zuciyarsu ta baci,duk wani abinda irinsu suka yi sai ace daidai ne ba wata matsala.
Abuna biyu kuma shi ne duk wani abinda suka son a yi masu daya jibanci kudin nan da nan za ayi masu, ko kuima a basu ahaka za a basu.
Saidai kuma wani abu sannu a hankali idan har aka cigaba da irin wannan hali na sangarta ‘ya’ya,su zama ‘yan lele ba a son fada masu duk wani abinda zai bata masu rai.
Yau da gabe sai Allah domin kuwa babu wani abinda ke dauwama sai ikon Allah,komai na iya sauyawa ba tai fadawa mutum za a yi ba cewa ga lokacin da al’amarin zai kasance ba.Wasu sai a bata su da kullum jin dadi ba tare da nuna masu hanyoyin da ake samun kudin ba,ba a koya masu sana’a, zuwa makaranta ma ba a matsa masu su je.
Har da idan ta Allah ta kasance ko sauyawar rayuwar kamar yadda na riga na yi bayani ido ya fara raina fata.Ko dai na gaba ya koma baya wanda daga haka ne abubuwa ske sauyawa ga wadanda aka kwadaitawa kullum dadi sai kashe kudi.
Baa san yadda za a nemo su ba amma an san hanyar kashewa, tun da dai an saba da dadin wahala ta shigo, dole ne a shiga aikata abubuwan da basu dace ba , domin dai kawai aji dadi.
Irin wadannan ‘ya’yan da aka sangarta daga karshe da idan ba sa’a ce aka yi abinda ba a so ne ya kan faru na aiakata abubuwan da basu dace, wanda kuma a lokacin wankin Hula ya kai dare babu wani gyaran da za a yi, domin kuwa icce ya kai ga rike wa ya yi girma, idan aka yi kokarin yin wani abu karaya shi za a yi.