Itatuwan Zaitun sun shafe shekaru a duniya ana afamani da su, ya fito ne daga yankin Asiya da kuma yankin Asiya ta tsakiya, sai kuma a wasu sassa na Afirika.
Ana shuka zaitun ne a yanzu, domin samun kudaden shiga, musamman ganin cewa, ana samar da ingantaccen irin da ya kamata don yin kasuwancinsa.
Kasashen da ke kan gaba wajen samar da man zaitun mai dimbin yawa a duniya sune; Sifaniya da Italiya da Greece da Siriya da Moroko da Turkiya da Masar da kuma Tunisiya, musamman ganin cewa, su ne kasashen da suka fi yin amfani da shi wajen kiwon lafiyar jikin dan’adam.
Har ila yau, bishiyar zaitun na jurewa ko wane irin yana yin da aka shuka ta, ya danganta da irin nau’in irin na zaitun da aka shuka.
Misali, nau’in irin zaitun da ake kira Kalamata, na fara yin ‘ya’ya ne a cikin shekaru hudu, har ila yau kuma ana da matkar bukatar man zaitun da ya kai kimanin kashi 80 zuwa kashi 90 a cikin dari.
Akasari, Musulmai ne shuka fi yin afnai da man zaitun, musamman wajen kiwon lafiya, inda buktar yin amfani da shi don kiwon lafiya ya kara karuwa a duniya.
Gyran Gona:
Ana bukatar manomin ya tabbatar da cewa, kasar noman da zai shuka irin na zaitun, ta kasance ta bushe kuma tana dauke da sanadarai da za su taimaka masa wajen saurin girma.
Ana kuma son ka da manominsa ya shuka irin a wajen da ake samun ruwa mai yawa domin yin hakan, zai ia hana masa saurin girma.
Yadda Ake Shuka Zaitun:
Ana shuka zaitun ta hanya biyu, ko a shuka irinsa kai-tsaye ko kuma a saro wani sashi a dasa, inda kuma a yayin shukar, ake bukatar manomin ya kasance ya bar tazara kamar mita biyar ana kuma fara shuka irin zaitun ne daga watan Afirilu zuwa watan Mayu.
Yi Masa Ban-ruwa:
Zaitun na jure wa kowane irin yanayi na kakar shuka, inda kuma ake bukatar manominsa, ya dinga yi msa ban-ruwa akai-akai, amma a lokacin kakar damina, ba sai an yi masa ban-ruwa akai-akai ba.
Har ila yau, ba a son manominsa ya yi masa ban-ruwa a satin da yake shirin fara dibansa.
Ana Zuba Masa Takin Zamani:An fi son a dinga zuba masa takin zamani samfarin NPK ko kuma a zuba masa takin gargajiya da ke dauke da sanadaran da zai sa shi saurin yin girma haka ba a son manominsa ya zuba masa taki gab da jijiyarsa don gudan ka da ya samu wata nakasa.
Kare Shi Daga Harbin Kwayoyin Cuta:
Ana son a dinga yi masa feshi don kare shi daga kamuwa da cututtuka.
Ribar Da Ake Samu A Noman Zaitun:
Manomansa na samun dimbin riba mai yawa tare da samun riba mai yawa, musaman idan sun fitar da mansa zuwa kasashen duniya don sayarwa.
Bishiyar zaitun za ta iya samar da kiligiram daga sha biyar zuwa ashirn a kowacce shekara.
Har ila yau, bishiyar zaitun, za ta iya samar da litocinsa ta mansa masu yawa a shekara.
Lokacin Dibansaa:
Idan har ya kai iya tsawon girmansa ana son a debe shi, inda kuma ake bukatar a yayin dibansa, a bi a hankali don kiyaye shi daga lalace wa, ganin cewa a lokacin, bai da wani kwari.
Jinkiri wajen dibansa, zai iya shafar dandanonsa,saboda haka,
dibansa a lokacin da ya dace, zai say a samu dandano mai dadi.