Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi shugaba Bola Tinubu da iyalinsa wajen kassara Nijeriya.
Wannan na cikin wata sanarwar da mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya raba wa manema labarai.
- Majalisar Jihar Kebbi Ta Amince Da Ƙudirin Gyaran Dokar Ƙananan Hukumomi
- Ambaliya: Yari Ya Bayar Da Tallafin Tiirela 15 Na Hatsi Da Wasu Kayayyaki A Zamfara
Ya ce illar da Tinubu ya yi wa Nijeriya, ko ya bar mulki, gyaranta zai yi matukar wahala.
Atiku, ya zargi shugaban kasar da hada mulkin da ya ke jagoranci da harkokin shi na kasuwanci, kamar yadda wani kamfaninsa a Legas ke karbar kudaden harajin gwamnati da ake kira Alpha Beta, yanzu haka ya fara aikata haka a matakin Gwamnatin Tarayya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, ya bayyana takaicinsa kan yadda Tinubu ya mayar da wani sashe na kamfanin NNPC karkashin kamfanin dan uwansa, Wale Tinubu na Oando.
Atiku, ya nuna damuwarsa a kan sake shirin sayar da kamfanin NNPC domin ba shi damar sake saye hannayen jarinsa, inda ya bayyana shi a matsayin wani yunkuri na mamaye kamfanin da wasu fitattun mutanen da ke kusa da Tinubu ke shiryawa.
Atiku, ya ce a watan Oktoban 2022, watanni biyar kafin zabe, kamfanin NNPC ya sanar da kulla yarjejeniya da Oando domin karbe gidajen man, duk da cewa NNPC na da gidajen mai 550 a sassan kasar nan, yayin da Oando ke da 94 kacal.
Ya ce wannan yarjejeniyar ce ta sanya shugaban kasa sake bai wa shugaban NNPC Mele Kyari sabon wa’adi duk da rashin kwarewarsa, yayin da ya kuma nada tsohon mai gidansa a kamfanin Mobil, Pius Akinyelure a matsayin shugaban majalisar gudanarwar NNPC.
Atiku, ya ce Gwamnatin Tarayya ta biya Wale Tinubu makudan kudin kafin karbar gidajen mansa, matakin da ya bayyana shi a matsayin haramcacce.