Bayanin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na kamanta yanayin da ya haifar da mutuwar Alhaji Isa Bawa, Sarkin Gatawa, ya jawo suka daga masu zargi.
Masu sharhin sun ce jawabin nasa ya mayar da hankali ne kan “yanayi” maimakon zargi kai tsaye ga masu kisan wanda hakan yana rage mahimmancin lamarin. Sun kuma bayyana damuwa game da amfani da kalmar “yan banga,” da ake yi, suna ganin cewa ya kamata ana ɗaukar su a matsayin ‘yan ta’adda saboda ayyukansu na kashe-kashe da fyade.
- Tinubu da iyalinsa na neman kassara Nijeriya — Atiku
- Yaushe Za A Ceto Mu Daga Masu Garkuwa Da Wutar Lantarki?
Masu yin wannan sharhi dai sun ce kiran su da “yan banga” bai bayyana girman barazanar da suke yi ba.
A jihohin kamar Zamfara, waɗannan ƙungiyoyin ta’addanci suna gudanar da ayyuka kamar karɓar haraji da kuma iko da wasu yankuna, wanda ya fi dacewa da ‘yan tawaye.
Haka kuma, suna ganin shirye-shiryen sulhu da ake yi sun gaza, domin yawancin su suna komawa cikin ta’addaci bayan ɗan lokaci.
Masu zargin sun kara jaddada cewa waɗannan masu laifi suna amfani da fasahar zamani, ciki har da kafafen sada zumunta, don yaɗa tsoro da tsara hare-hare.
Kasartuwarsu a yanar gizo zai iya bayar da dama wajen bin su da kuma daƙile ayyukansu idan gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace.
Ana ƙara neman gwamnati ta na kiran waɗannan ƙungiyoyi a matsayin ‘yan ta’adda kuma ta ɗauki matakai masu ƙarfi don shawo kan tashin hankali da ke addabar wasu jihohi a ƙasar.