Darakta Janar ta Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, ta soki ‘yan siyasar Nijeriya da amfani da rashin tsaro wajen yaki da ‘yan adawa domin cimma wata manufa ta siyasa.
Da take jawabi a taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Nijeriya na shekarar 2024 a Legas ranar Lahadi, Misis Ngozi ta koka da cewa, amfani da rashin tsaro a matsayin makami, zai kara tsananta kalubalen kasar.
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Fiye Da 200 A Kaduna – SEMA
- ‘Yan Boko Haram Na Ci Gaba Da Tuba A Kasar Nijar
A jawabinta mai taken: ‘Mu’amalar zamantakewa domin inganta makomar Nijeriya a gaba’, Misis Ngozi ta jaddada muhimmiyar alaka tsakanin tsaro da cigaban tattalin arziki.
Ta soki ’yan siyasa kan haifar da rashin tsaro don lalata mutuncin abokan hamayyarsu, ba tare da la’akari da darajar dan’Adam ko asarar dukiya ba.
“Dukkanmu mun san cewa, ‘yan siyasa sun yi amfani da kawo kalubalen tsaro a kasarmu don dalilai na siyasa, wanda hakan ya haifar da wani bangare na kuncin rayuwa da muke ciki a yanzu.
“Muna da ‘yan siyasa da suka yi imanin cewa, hanya mafi kyau da za su bata gwamnatin abokan hamayyarsu, ita ce, tada zaune tsaye, ta yadda mutane za su debe kyakkyawan zato ga gwamnatin, ba tare da la’akari da cewa, matakin ka iya kai wa ga asarar rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba. Dole a dakatar da irin wannan tunani,” in ji Misis Ngozi Okonjo-Iweala.
A don haka, Misis Okonjo-Iweala, ta yi kira da a yi amfani da fasahar da ake da su wajen yaki da satar man fetur da kuma hukunta masu laifi, inda ta ce, dole ne a daina satar dukiyar kasa.