Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Nijeriya (NCoS), ta bayyana cewa fursunoni 274 ne suka tsere daga gidan gyaran hali na New Prison da ke Maiduguri a Jihar Borno.
Wannan na zuwa ne bayan da wani bangare na katangar gidan yarin ya rushe sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta auku a birnin.
- NiMet Ta Yi Hasashen Tsawa Ta Kwanaki 3 Daga Talata
- Ambaliya: Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Agaji A Borno
Kakakin hukumar, Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ambaliyar ruwan ta samo asali bayan fashewar dam ɗin ruwa naAlau, wanda ya mamaye sassa daban-daban na birnin.
Lamarin da ya raba kusan mutane miliyan biyu da gidajensu tare da hallaka wasu da dama.
Kazalika, ya ce fursunoni 281 sun tsare ne a lokacin da jami’an ma’aikatar tare da tallafin wasu jami’an tsaro ke kokarin kwashe su zuwa wani gidan yarin mafi tsaro sakamakon rushewar katangar.
Hukumar ta ce, suna da cikakken bayanan daukacin fursunonin da suka tsere har da hoton yatsunsu.
Abubakar, ya ce tuni suka kama fursunoni bakwai daga cikin wadanda da suka tsare.
Ya ce yanzu haka suna aiki da sauran jami’an tsaro domin gano sauran wadanda suka tsere.