Majalisar Dinkin duniya ta bai wa Jihar Borno tallafin dala miliyan shida domin taimaka wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.Â
Majalisar ta ce ana bukatar akalla dala miliyan 148 domin ci gaba da gudanar da aikin agaji a Maiduguri.
- TY Ɗanjuma Ga Hafsoshin Tsaro: Babu Sauran Wani Uzuri, Ku Kawo Ƙarshen Kashe-kashe Kawai
- Ambaliya: Muna Da Bayanan Fursunonin Da Suka Tsere A Maiduguri — Hukuma
Shugaban hukumomin jin-kai na mjalisar a Nijeriya, Mohammed Fall ne, ya gabatar da wadannan alkaluma a dai-dai lokacin da ake ci gaba da aikin jin-kai a jihar.
Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Steffan Dujjaric, ya ce wakilan hukumomin jin-kai na majalisar tare da na kungiyoyin fararen hula da kuma na kungiyar agaji ta Red Cross sun ziyarci birnin domin tantance bukatun jama’a.
Dujjaric ya ce tawagar ta gana da mutane da dama da iftila’in ya shafa baya.
Jami’in ya ce majalisar tana raba dafafen abinci da ruwan sha ga jama’a, tare da amfani da jirgin sama wajen kai wa ga wadanda ke makale a yankunan da ambaliyar ba ta janye ba.
Idan ba a manta ba a makon da ya wuce ne ambaliyar ruwa ta daidaita birnin Maiduguri sakamakon ballewar dam din ruwa na garin Alom.