Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 23 ga Satumba, 2024, domin yanke hukunci kan karar da ke neman tsige Dr. Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Idan dai za a iya tunawa, a zaman da aka yi a baya a ranar 5 ga watan Yuli, alkalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya sanya ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, da zai yanke hukunci kan karar amma ba a sanya karar ba a cikin jerin kararrakin da kotun za ta saurara ba a yau.
- Kasar Sin Za Ta Sanya Takunkumi Kan Kamfanonin Sojan Amurka Wadanda Suka Sayar Da Makamai Ga Yankin Taiwan
- Zaben Kananan Hukumomi: A Magance Maimaita Magudi A Jihar Kaduna
Da aka tuntube batun, an bayyana cewa, ba a shirya zaman sauraron karar ba a yau, kuma tuni magatakardar kotun ya sanar da wadanda ke cikin karar domin a dage ranar.
“Tuni mun kira masu shigar da kara da wadanda ake tuhuma ta wayar tarho domin sanar da su halin da ake ciki. mako mai zuwa, 23 ga watan Satumba, za a yi sabon zaman”.
Kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya karkashin jagorancin Saleh Zazzaga, ce ta shigar da kara ta hanyar lauyansu, Benjamin Davou, inda suka kalubalanci yadda aka nada Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC, ganin cewa, ba daga shiyyar Arewa ta tsakiya ya fito ba.