A ranar Asabar din nan ce, mutane a Jihar Edo ke fita rumfunan zabe domin kada kuri’unsu na zaben sabon gwamnan.
Zaben Gwamnan Jihar Edo ya kasance zakaran gwajin dafi da za a fafata a tsakanin manyan jam’iyyun Nijeriya, wanda zaben yake jan hankali a cikin fagen siyasar Nijeriya.
- Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa
- Dakta Gadan-ƙaya Ya Bada Haƙuri Kan Zargin Auren Jinsi Da Ya Yi A Bauchi
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsara gudanar da zaben Gwamnan Edo a ranar 21 ga Satumba, 2024.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Sam Olumekun, INEC ta sanya wannan rana domin tabbatar da shirye-shirye da kuma gudanar da zaben cikin lumana.
Ana sa ran masu kada kuri’a a fadin jihar za su fito da yawa domin zaben sabon gwamnan jihar.
Manyan ‘yan takara da za su fafata a wannan zabe sun hada da na jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, Asue Ighodal da kuma na jam’iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo.
Har ila yau, shi ma dan takarar jam’iyyar LP, Olumide Akpata zai bayar da mamaki a wannan zabe, ganin yadda jam’iyyarsa ta bayar da mamaki a zaben 2023.
Bisa kididdigar da INEC ta fitar na masu rajistar zabe, Jihar Edo na da masu kada kuri’a 2,501,318.
Kwamishiniyar ta Jihar Edo, Farfesa Rhoda Gumus ta sanar da cewa har yanzu masu rajistar zabe 373,030 ne suka kasa karbar katin zabesu a jihar.
Wannan adadi ya nuna yadda al’ummar Edo ke kara wayewa a siyasance, wadanda ke da sha’awar yin amfani da ‘yancinsu na dimokuradiyya.
INEC ta bayyana cewa, masu rajistar zabe guda 2,128,288 ne suka amshi katin zabensu. Wannan lamba wata alama ce mai muhimmanci na shirye-shiryen da masu zabe suke da shi game da zaben Jihar Edo.
Hukumar INEC ta tantance kungiyoyin fararen hula na cikin gida da na kasashen waje wadanda za su sa ido a wannan zabe.
Kungiyoyin dai sun yi kira ga ‘yan takara da magoya bayansu su kai zuciya nesa a lokacin gudanar da zabe domin samun damar yin sahihin zabe a Jihar Edo.
An dai jabge jami’an tsaron tun daga kan ‘yansanda da sojoji da jami’an hukumar farin kaya (DSS) domin jiran ko-ta-kwana.