An shiga cikin tashin hankali a wasu sassa na Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a ranar Lahadi biyo bayan kama wani da ake zargin shugaban kungiyar Boko Haram ne.
Wani gidan rediyo mai zaman kansa a Abeokuta ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi da yamma wanda ya haifar da firgici a tsakanin mazauna jihar.
- Rashin Tsaro: Sanatan APC Ya Nemi Monguno Ya Yi Murabus
- ISWAP Ce Ta Kai Wa Sojoji Hari A Dutsen Zuma – Rahoto
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar tsaro ta farin kaya sun kama wanda ake zargin ne a daren ranar Asabar.
Labarin ya bazu a shafukan sada zumunta na jihar a ranar Lahadi.
Lamarin dai na da nasaba da shirin kai hare-hare a wasu jihohin Kudu maso Yamma da ake zargin ‘yan ta’adda na shirin yi.
Sai dai wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilinmu cewa an kama wanda ake zargin shugaban kungiyar Boko Haram ne kwanaki a unguwar Ijaye da ke Abeokuta.
Majiyar ta ce tun da farko wanda ake zargin ya yi turjiya kafin ya mika wuya ta karfin tsiya ga jami’an DSS.
A cewar mai binciken, an gudanar da aikin ne a daren ranar Asabar.
A rahoton da gidan rediyon ya bayar, ya ce dan ta’addan da ake zargin ya isa Abeokuta ne daga Katsina, inda ya yi aikin tsaro a Ijaye, inda ya ke tattara bayanan sirri kan hare-haren ta’addanci.
Majiyar tsaron ta ce, “Shi (wanda ake zargin) ya koma Abeokuta ne domin ya kafa kungiyar ‘yan ta’adda domin yin garkuwa da mutane da kuma kai hare-haren ta’addanci.
“Kuma bayan wani taron sirri da aka yi, jami’an tsaro dauke da bindigogi sun kai farmaki maboyarsa sannan suka damke shi.
“Ba abu ne mai sauki ba. Amma da yardar Allah zamu shawo kan lamarin.
“Har yanzu akwai da yawa daga cikinsu, amma muna kan gabar aikinmu.”
Wakilinmu ya tattaro cewa wanda ake zargin yana hannun DSS har yanzu.
Da aka tuntubi kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, bai amsa sakon da aka aike masa ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce bai da masaniya kan lamarin.