Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), ta kama kwayar Tiramol sama da miliyan biyu da dubu dari bakwai, da aka yi yunkurin fita da ita kasashen waje daga tashar ruwan Apapa da ke jihar Legas.
A sanarwar da NDLEA ta fitar jiya Lahadi, ta ce kwayar na dauke ne a cikin katan-katan 55, da suka hada da nau’ikan Tapentadol da kuma Carisoprodol na Tiramol, da kudinsu ya kai Naira miliyan daya da dubu dari uku da saba’in da biyar.
Sashen BBC Hausa ya sanar da cewa NDLEA ta bayar da lambar kwantenar da: SUDU 7538656, inda ta ce ta samu bayanan sirri da suka tabbatar mata abin da ta ke dauke da shi.
Ko a makon da ya gabata an kama mutum biyar a tashar jirgin saman Murtala Muhammad da ke Ikeja a Legas din, yayin da suke yunkurin fitar da wasu nau’ukan kwaya zuwa birnin Landan da Dubai.