Bisa rahoton da aka samu na tattalin arzikin kasa, ya nuna habakar noma a Nijeriya ta ragu da kashi 1.4 cikin 100; sakamakon tabarbarewar rashin tsaro da tsadar kayan noma a wannan fanni na aikin noma a cikin zango na biyu na shekarar 2024.
A cikin shekara guda, fannin ya karu da kashi 1. 41 cikin 100 daga kashi 1.50 a cikin 100, wanda kuma fannin ya sake samun raguwa da kashi 0.09 a cikin 100 a shekarar 2023.
- Me Ya Sa Masu Noman Albasa Ke Samun Karamar Riba A Nijeriya?
- Zamfara: Yadda Zargin Juna Da Hannu A Ta’addanci Ya Yi Kamari Tsakanin Dauda Da Matawalle
Haka zalik, daga zango zuwa zango; fannin ya samu karuwa da kashi 0.18 cikin 100.
Babban jami’i a cibiyar kasuwanci mai zaman kanta, Muda Yusuf; a wata hira da ya yi da Jaridar BusinessDay, ya bayyana cewa; kalubalen rashin tsaro a kasar, shi ne babban matsalar da ke shafar fannin, wanda hakan ya tilasta wa manoma yin watsi da gonakinsu; inda hakan kuma ya kara haifar da hauhawar farashin kayan abinci a fadin kasar.
Muda ya yi nuni da cewa, sai a magance kalubalen rashin tsaro a wannan kasa; kafin a iya magance kalubalen hauhawar farashin kayan abinci.
Shi kuwa, wani kwararre a fannin aikin noma da bai bukaci a bayyana sunansa ba ya sanar da cewa, fannin na matukar fusknatar koma baya.
Har ila yau, wani rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ya nuna cewa, fannin na taimaka wa tattalin arizkin kasar da kusan kashi 22.61 cikin 100.
Sai dai, a fannin cikin zango na biyu na 2023, ya taimaka da kashi 23.01 cikin 100; wanda ya dara na zango na daya a 2024, da ya kai matsayin kashi 21.07 cikin 100.
Kola Aderibigbe, shugaban dangogin fannin aikin noma; kuma shugaban kungiyar kasuwanci da masana’antu, reshen Jihar Legas a wata hira da aka yi da shi a kwanakin baya ya ce, “A yanzu, manoma na daukar hayar jami’an tsro masu zaman kansu ne, domin kare gonakinsu da amfanin da suka shuka da kuma kawunansu”.
Haka zalika, wani rahoton sirri na (SBM); wanda yake mayar da hankali kan kasuwar Afrika da kuma fannin tsaro ya bayyana cewa, daga 2020 zuwa 2024; sama da manoma 1,356 ‘yan bindiga suka hallaka a Arewacin Nijeriya, wanda hakan kuma ya jawo gaza yin noma tare da haifar da hauhawar farashin kayan abinci da kuma dakatar da masu son zuba jari a fannin.
Shi ma babban jami’i a kamfanin tuntuba na akin noma Florunsho Olayemi Sammorf ya sanar da cewa, “Duk hekta guda ta noma yanzu ta rubunya, wanda ya ce; hakan ya sanya manoma rage yawan hektar da suke nomawa kari kuma da kalubalen rashin tsaro, inda hakan ya kara jawo hauhawar farashin kayan abinci”.
Fannin aikin noma na wannan kasa, shi ne kan gaba wajen samar da kashi 87.48 cikin 100, wanda ake samun akalla Naira tiriliyan 9.8 a zango na biyu na 2024.
Bugu da kari, a kwanakin baya; hukumar samar da abinci da harkar aikin noma ta duniya (FAO) ta sanar da cewa, ‘yan Nijeriya sama da miliyan 31.8; na fuskantar karancin abinci, wanda hakan ya jawo rashin samun abinci mai gina jiki, musamman a tsakanin mata da yara a daukacin fadin wannan kasa.
Har ila yau, a cikin wani rahoton na kungiyar ‘Cadre Harmonise’ da ke sa ido a kan samar da wadataccen abinci da ta fitar bisa hadaka da hukumar kasuwanci ta kasa da kasa ta ‘GIZ’ da ke da shalkwata a Kasar Jamus sun nuna cewa, an samu hauhawar farashin kayan abinci, sakamakon cire tallafin iskar gas da kuma fuskantar kalubalen rashin tsaro, wanda hakan ya jefa ‘yan Nijeriya cikin halin kuncin rayuwa.
Har ila yau, Nijeriya na fuskantar mummunar hauhawar farashin kayan abinci da ya kai kashi 40 cikin 100 a wannan shekara ta 2024 tare da koma baya a bangaren noma da kuma fuskanta tsadar kayan aikin noma.