Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ƙarin buhunan shinkafa dubu 18,500 ga jihar Kebbi a ƙoƙarin gwamnatin tarayya na tallafawa marasa galihu a cikin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.
Wannan tallafi zai amfanar da mutane har 18,500, kowannensu zai karɓi buhun shinkafa mai nauyin kilo 25 guda daya.
- NAPTIP Ta Kuɓutar Da Yara 19 Da Aka Sace A Kebbi
- NUJ Ta Taya Gwamnan Kebbi Da Nijeriya Murnar Cika Shekaru 64 Da Samun ‘Yancin Kai
Ministan Ma’aikatar gona da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ne ya jagoranci rabon kayan abinci a birnin Kebbi, wanda Gwamna Nasir Idris da Ministan kasafin kudi da tsare-tsare tattalin arziki Sanata Abubakar Atiku Bagudu da babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa ga shugaban ƙasa Alhaji Kabiru Ibrahim Masari suka taimaka masa yayin gudanar da bikin kaddamar da rabon.
A cewar, Abubakar Kyari, Shugaba Tinubu ya gamsu da yadda Gwamna Nasir Idris ya ke jajircewa wajen inganta yanayin rayuwa da aikin noma da samar da abinci a jihar Kebbi.
Minista Abubakar Atiku Bagudu ya yaba da kwazon Gwamna Idris, inda ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya jajirce wajen tallafawa jihohi domin samun nasara.
Gwamna Nasir Idris ya nuna jin dadinsa ga shugaba Tinubu kan taimakon da ya yi masa, inda ya yaba da gagarumin tasirin tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa.