Shafin Taskira shafin ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yawan samun jirgin ruwa a Nijeriya, shin me ke kawo hakan? Hassan Tijjani
- Yawaitar Ambaliyar Ruwa: Ina Mafita?
- Yadda Bukukuwan Sallah Suka Kasance A Garuruwanmu – Mabiya Taskira
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu!
Abubuwan da yake kawo yawan haduran jiragen ruwa a Nijeriya shi ne, suna daukar mutane da yawa a cikin jirgin, wato mutanen da yawansu ya fi karfin jirgin kamar misali a ce jirgin da zai dau mutum 20 sai ki ga sun dauki mutum fiye da haka sai su dauki 30 ko ma fiye da haka to kin ga an yi wa jirgin yawa, ya yi nauyin da zai iya nitsewa da mutane a ciki.
Sannan kuma sai yawan ruwa da ake samu da damina ba mu da fadamun ruwa isassu a Nijeriya saboda za ka ga a haka ma ana rufe fadamu ana gidaje a kai to inda mu can zai je sai ruwa ya samu ya tare a waje guda sai ki ga ruwa ya cika sosai to cikar wannan wajen ruwan shima kokiyar ruwa za ta iya tsinkewa ta kifar da jirgi.
Abubakar Tijjani
Hadarin jirgin ruwa na faruwa ne saboda matsaloli guda biyar, wannan matsalolin sun hada da:
1. Yanayi
Yanayi wato yana cikin abin da yake janyo wa hadarin jirgin ruwa saboda ruwan sama, in ana ruwa kogi ya kan cika ya batse, hakan zai sanya in ana tafiya a cikin jirgin saboda karfin ruwa sai jirgin ya fara kifewa ko ya lume
2. Ambaliya
Ambaliya a Nijeriyai na daga cikin abin da yake janyo yawan hadarin jirgin ruwa, duba da yanayin rashin magudanar ruwa da ruwa za rika wucewa, da ruwan Dam da ake saki daga kasashrn da muke makotaka da su wanda yake ratsa gonaki don samun wurin wucewa zuwa kogi, karfin ruwan da yawansa ya kan saka jirgi ya kife, misali, ambaliyar da aka yi a Borno.
3. Rashin ba wa jirgin kulawa wajen gyara
Wannan wata matsala ce da kan iya haifar da faruwar jirgi ya karye ko ya ruguje in an hau, musamman in an masa nauyi
4. Gudu
Gudu na cikin abin da ke janyo yawan hadari a jirgin ruwa, in ana gudu a jirgin ruwa, jirgin ya kan zama bashi da nauyi wanda dan juyi za’a yi kadan ya saka jirgin ya kife
5.Rashin iyawa/Operator inedperience
Rashin gogewa kan tuka jirgin rawa kan haifar da matsaloli da dama kamar jirgi ya kife, jirgi ya tsaya a tsakiyar ruwa, jirgi ya nitse da sauransu.
Rabi’atu Abdullahi Muhammad
To abin da yake janyo hadarin jirgin ruwa shi ne, rashin isassun wajen da ruwa zai tsaya wato fadamomi sun yi kadan kasancewar yawanci ana rufe fadama a yi gida a kai to da zarar an yi ruwan sama sai yabi daji ya shiga kogi, sannan ga Dam shima idan ya cika suka ga zai musu barna suma su sake shi to dagana kogi ya cika to wannan ma zai iya kawo hadarin jirgin ruwa.
Sannan suma masu jirgin ruwan da kansu su kan zama sanadiyar yi saboda daukan mutanan da su kafi yawan da aka tsara jirgin zai dauka kamar idan zai dau mutum goma sai a sama masa 20 ko fiye da haka to da zarar jirgin ya yi kasa dama gashi kogi ya cika abu kadan ne sai ki ga hatsri ya faru wanda za ki ga wani tsabar ya yi nauyi na ciki suna saka hannunsu cikin ruwan saboda ya yi kasa suna ciki suna dan ban ruwan.
Muhammad Abdullahi
Assalamu alaikum!
Abubawan da yake kawo hadarin jirgin ruwa su ne, rashin isassun jirage ko na ce rashin jirage masu kyau, ko kuma rashin kulawa da su akai-akai, sannan sai daukar mutane da yawa wadanda suka fi karfin jirgin, sannan sai cikar ruwa da damina ruwa ya cika ya yi karfi sosai, to idan kokiyar ruwa ta tsinke jirgi na saman ruwa to za ta iya nitsar da shi. To abubuwan dai da yawa ga su duka sai dai Allah ya kara tsarewa.
Habiba Tijjani
Assalamu alaikum!
Abubuwan da suke kawo hadarin jirgin ruwa a Nijeriyai suna da yawa:
Samun ruwan sama mai yawa da damina saboda idan aka samu ruwa sosai da damina kogi zai cika duba da karancin wurin da ruwa yake zama dole kogi yake tafiya, sannan kuma muna da Dam suma can idan suka cika suka ga zai musu barna sakin sa suke yi imma ya yi kogi ko ya yi gari to wannan ya kan janyo hadarin jirgin ruwa saboda kogi ya cika ruwa ya yi karfi.
Sannan sai hada ma ta masu jiragen ruwan ba za su dauki mutane daidai yadda aka ce jirgin zai dauka ba sai sun yi kari sun dauka da yawa to nauyi ma yana iya kawo hadarin jirgin ruwa saboda jirgin zai yi kasa sosai yana tangal-tangal. Allah ya kawo mana sauki.