Jaridar “The Nation” da ake wallafawa a Najeriya, ta wallafa wani bayani mai ban sha’awa a kwanan baya, mai taken ”Bayan aiki mai inganci na kwashe ‘yan kasa da kasar Sin ta yi”, wanda ya ce, bayan tsanantar yanayin yakin da ake yi tsakanin Isra’ila da Lebanon, gwamnatin kasar Sin ta kwashe ‘yan kasar fiye da 200 daga kasar Lebanon cikin wasu kwanaki 2 zuwa 3, har da iyalansu ‘yan wasu kasashe daban daban. Kana sabanin ingantaccen matakin da kasar Sin ta dauka, kasar Amurka, da ta kan soki sauran kasashe, ta fakewa da batun ”kare dimokuradiyya da ‘yancin dan Adam”, ta ki daukar matakin janye Amurkawa daga Lebanon, inda a maimakon haka, ta bukaci Amurkawan dake Lebanon da su sayi tikitin jirgi da kansu don barin kasar. Wannan yanayi na ko-in-kula da gwamnatin kasar Amurka ta nuna ya bakanta ran dimbin ‘yan kasar, har ma sun rubuta a shafin yanar gizo mai dauke da labarin, cewa ”Kamar bai ishe su ba su yi amfani da kudin jama’a wajen kashe ‘yan kasar Lenanon, yanzu ko ‘yan kasar Amurka ma za su fara kashewa.”
Sa’an nan an bayyana a cikin wannan bayani cewa, ta hanyar kwatantawa, za a iya ganin yadda kasar Sin ke kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta, gami da karfin kasar na kubutar da ‘ya’yanta da abokanta daga yanayi mai cike da hadari.
- Magoya Baya Sun Kori Kwankwaso Daga NNPP, Sun Kona Jar Hula A Jihar Neja
- Gwamnatin Sakkwato Ta Kafa Kwamitin Da Zai Fara Sayar Da Kayan Abinci Masu Sauki
Hakika, idan mun kwatanta sakamakon da aka samu a kasar Sin da na Amurka, ta fuskar tinkarar dimbin abubuwan da suka auku ba zato ba tsammani, za mu iya ganin yadda ake samun bambanci sosai tsakanin kasashen 2. Misali, tun daga watan Satumba har zuwa farkon watan da muke ciki, dukkanin kasashen 2 wato Sin da Amurka sun taba fuskantar mahaukaciyar guguwa guda 2. Kana a cikinsu wata guguwar da ta aukawa babban yankin kasar Sin ta fi sauran 3 karfi. Amma a karshe an samu daruruwan mutanen da suka rasa rayuka a kasar Amurka sakamakon bala’in guguwa, yayin da adadin bangaren Sin mutum 6 ne kacal.
To ko me ya sa ake samun wannan babban bambanci? Hakika kasar Sin ta shirya sosai kafin zuwan guguwar, inda aka rufe makarantu da wuraren yawon shakatawa cikin gaggawa, da kwashe mutane fiye da dubu dari daya zuwa sauran wurare, da shirya kayayyakin da ake bukata wajen tinkarar bala’i, gami da sanya sojoji su kimtsa don gudanar da aikin ceto daga bisani. Sa’an nan bayan da bala’in guguwa ya auku, sojoji da ‘yan kwana-kwana, da fararen hula sun yi hadin gwiwa a kokacin maido da hidimomin samar da ruwa, da wutar lantarki, da sadarwa, cikin sauri. Bayan wasu kwanaki, an kai ga gyara yawancin kayayyakin more rayuwa da suka lalace.
Sa’an nan a kasar Amurka, abun da ya faru shi ne, ba a kimtsa sosai tun kafin aukuwar bala’in ba. A cewar Zhou Deyu, wani masanin ilimin harkar siyasa, da ya samu digiri na 3 a jami’ar Pittsburgh ta kasar Amurka, ba a son daukar matakan kandagarkin bala’i a kasar Amurka, saboda yin haka zai janyo suka daga ‘yan siyasa abokan gaba, su rika cewa wai ana rigakafi fiye da kima, da salwantar da kudin jama’a. Ban da haka, ‘yan siyasan kasar na son zuba kudi bayan aukuwar bala’i, ta yadda jama’a za su yi musu matukar godiya, maimakon kare jama’a daga tasirin bala’i tun da farko. Sa’an nan, yadda ba a kimtsa sosai tun kafin abkuwar bala’i ba, ya haddasa karancin kudin da ake bukata don gudanar da aikin ceto da ba da tallafi, bayan da bala’in ya auku.
An ce kusan wasu makonni 2 bayan aukuwar bala’in guguwa, gwamnatin Amurka ta samar da dala miliyan 30 da wani abu don gudanar da aikin ceto. Yayin da a dayan bangare, a ranar da bala’in guguwa ya auku kadai, kasar Isra’ila ta tabbatar da damar samun tallafin aikin soja na dala biliyan 8.7 daga kasar Amurka.
Idan an yi bincike kan dalili na tushe, wanda ya sa ake samun bambancin tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a fannin kula da wasu batutuwan da suka abku ba zato ba tsammani, to, za a ga ya shafi tunanin masu gudanar da mulki na kasashen 2. A kasar Sin, daya daga cikin tunanin mulki masu muhimmanci na gwamnatin kasar shi ne mai da moriyar jama’a gaban komai, da kokarin bautawa jama’a. Wannan tunani ya sa kasar yin iyakacin kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a yayin da ake fuskantar bala’i, da tallafawa marasa karfi, da kokarin kawar da talauci bayan yanayin tattalin arzikin kasar ya inganta, gami da neman raya bangarorin horaswa, da rage talauci, da samar da guraben aikin yi, yayin da take hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, don sanya zamanantarwar nahiyar Afirka amfanin al’ummunta. Kana a nata bangare, manyan kusoshi masu ikon mulki na kasar Amurka, sun fi dora muhimmanci kan moriya a fannin siyasa. Misali, ginshikin mamban jam’iyyar Republican ta kasar Amurka Lindsey Graham, ya fada wa kafofin watsa labarun kasar cewa, idan an kwatanta da aikin ceton jama’ar kasarsa da bala’in guguwa ya ritsa da su, aikin tallafawa kasar Isra’ila don ta ci gaba da gudanar da yake-yake ya fi muhimmanci.
A cikin bayanin da jaridar the Nation ta wallafa, editanta ya mai da hankali kan karfin da wata kasa ta nuna, ta hanyar gudanar da aikin kwashe ‘ya’yanta daga sauran kasashe. Sai dai a gani na, wani abun da ya fi muhimmanci, da dacewa da lura, shi ne yadda wata kasa ke kula da ‘ya’yanta. Saboda idan wata kasa ba ta taba dora muhimmanci kan rayukan jama’arta ba, to, ta yaya za ta kula da jama’ar sauran kasashe? (Bello Wang)