Rikicin gida a jam’iyyar PDP na daukar wani salo na daban, wanda a yanzu haka lamarin ya kazance, inda gwamnoni 9 daga cikin 13 na PDP da wasu jiga-jign jam’iyyar suka goyi bayan dakatar da shugaban riko na kasa na jam’iyyar PDP, Ambasada Umar Damagum.
Sobon rikicin ya kunno kai ne tun lokacin da wani bangare na jam’iyyar a wata sanarwa da Debo Ologunagba ya fitar, ya bayyana cewa ya dakatar da shugaban riko na kasa da kuma sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu.
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
- Mambobin Kungiyar SCO Sun Bayyana Adawa Da Matakan Kariyar Cinikayya
Dakatarwar ya janyo cece-kuce a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar, inda a yanzu haka masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na nemo hanyar dinke bakin zaren.
Sai dai a sanarwar Ologunagba da ya fitar, ya ce an dakatar da Damagum da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Anyanwu, saboda cin amanan jam’iyyar.
Ya ce an dakatar da su biyun ne saboda wasikar da suka aike wa kotun daukaka kara mai lamba: CA/PH/307/2024, kan matsayin jam’iyyar a shari’ar da ta shafi tsofaffin ‘yan majalisar dokokin Jihar Ribas su 27 da suka suka bar kujerunsu bayan sun fice daga PDP zuwa APC.
“Saboda haka, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya yi amfani da sashi na 57, 58 da 59 na kundin tsarin mulkin PDP wajen dakatar da Amb. Illiya Damagum da Sanata Samuel Anyanwu a matsayinsu na shugaban riko na jam’iyyar na kasa da kuma sakataren jam’iyyar na kasa tare da mika su ga kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar domin daukar mataki.
“A halin yanzu, an dakatar da jami’an biyu daga dukkan tarurrukan jam’iyya da ayyuka na jam’iyyar har sai an kwamitin ladabtarwa na kasa ya kammala bincike,” in ji shi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnoni 9 na PDP sun amince da dakatar da Damagum daga mukaminsa na shugaban rikon jam’iyyar.
A cewar rahotanin, gwamnonin su ne Siminalayi Fubara (Jihar Ribas); Douye Diri (Jihar Bayelsa); Godwin Obaseki (Jihar Edo); Sheriff Francis Orohwedor Oborebwori (Jihar Delta); Agbu Kefas (Jhar Taraba); Dauda Lawal (Jihar Zamfara); Peter Mbah (Jihar Inugu); Ademola Adeleke (Jihar Osun) da Fasto Umo Eno (Jihar Akwa Ibom).
Rahotannin sun ce matakin ya biyo bayan wani taro da aka gudanar a ranar Asabar, inda gwamnonin suka amince da nadin Alhaji Ahmed Alaghi, ma’ajin jam’iyyar PDP na kasa a matsayin sabon shugaban riko na jam’iyyar.
An ruwaito cewa wani hadimi daga cikin gwamnonin yana jaddada kudirin gwamnonin na mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP da kuma warware rigingimun cikin gida ta saukakkiyar hanya.
Ya kara da cewa gwamnonin sun sake jaddada aniyarsu na gina jam’iyyar PDP da hadin kai tare da fifita muradun jam’iyyar sama da ra’ayin wani.
Sai dai mukaddashin jami’in yada labarai na jam’iyyar PDP, Ibrahim Abdullahi, ya karyata goyon bayan gwamnonin.
Ya ce wannan magana babu kamshin gaskiya a cikinta, babu wasu gwamnoni biyu da suka yi Magana ballantana a ce har gwamnoni 9 sun amince da wannan dakatarwar.
Tun da farko dai, jam’iyyar ta shirya gudanar da taronta na kasa a ranar 24 ga watan Oktoba, domin zaben sabon shugaban jam’iyyar na kasa wanda zai kammala wa’adin tsohon shugaban, Dakta Iyorchia Ayu.
Ana sa ran Damagum zai koma matsayinsa na baya na mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa bayan kammala zaben.
Amma wata babbar kotun tarayya ta hana kwamitin gudanrwa da kwamitin zartarwa na PDP tsige shugaban riko na jam’iyyar. Sai dai kuma ba a saka kungiyar gwamnonin PDP cikin wannan hukuncin kotun ba.
Majiyoyi sun nuna cewa gwamnonin PDP na ta lalubo hanyoyin warware rikicin.
Wani jigon jam’iyyar da ya nemi a sakaye sunansa ya ce masu ruwa da tsaki a shiyyar arewa ta tsakiya ba za su iya jurewa abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar na nuna son kai da kuma bujirewa tsarin mulkin jam’iyyar dangane da batun tsarin karba-karba a tsakanin shiyya-shiyya.
A cewarsa, babban abin da ‘ya’yan jam’iyyar PDP suka tsayu a kai shi ne, dole ne a karbo kujerar shugaban jam’iyyar daga wurin Damagum a mayar wa yankin arewa ta tsakiya.
Shi ma wani jigo a jam’iyyar, wanda kuma ya taba zama shugaban majalisar dokokin Jihar Filato a lokaci guda, Hon. Istifanus Mwansat, ya bai wa dattijai da dukkan shugabannin jam’iyyar da su tashi tsaye wajen gudanar da bin tsarin karba-karba a shugabancin jam’iyyar.
Sai dai kuma wasu ‘yan majalisar PDP sun bayyana matukar damuwarsu kan makircin tare da zargin APC da gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu kan kokarin mayar da Nijeriya tafarkin tsarin kasa mai jam’iyya daya.