An bukaci gwamnatin tarayya ta inganta sake habaka harkokin amfanin gona, domin samun damar fitar da shi zuwa kasashen waje, kana gwamnatin ta fi mayar da hankali kan gudanar da ayyukan da za su kara habaka fannin; baya ga man fetir da kusan shi kadai ake iya fitar da shi zuwa kasashen na ketare.
Wasu kwararru ne suka bayar da wannan shawara, a taron shekara karo na tara; a wajen baje kolin da bankin Zenith ya shirya.
- Kashi 67 Cikin 100 Na Ɗaliban Kaduna Sun Samu Nasara A WAEC – Kwamishinan Ilimi
- Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnoni Na Tozarta Dimokuradiyya – Jam’iyyun Adawa
Taken taron shi ne, ‘Fitar da kayan amfanin gona zuwa kasashen, baya ga man fetir; domin kara farfado da fannin’.
Sun sanar da cewa, Nijeriya za ta iya amfana da kashi 70 na yawan matasan da ke kasar ta hanyar hada-hadar musaya.
Daya daga cikin kwararrun, Obiora Madu ya ce, “Kashi 70 na yawan al’ummar Nijeriya, matasa ne; wanda hakan ya sanya muke da karfin da za mu iya gudanar da ayyuka masu yawan gaske a kasuwar duniya”.
Madu ya kara da cewa, akwai bukatar kara wayar da kai; domin fadakarwa a kan ayyukan fitar da kaya zuwa kasashen ketare, musamman a kan amfanin gona.
Wata kididdigar tattalin arzikin kasar a zango na biyu ta yi nuni da cewa, jimillar kayan da ba su shafi fannin mai fetir a Nijeriya ba a 2024, ta kai dala 1.2, daidai da Naira biliyan 1.8, wanda hakan ya nuna cewa, ta kai yawan kashi 9.28 na jimillar kayan da aka fitar a cikin wannann shekara.
Haka zalika, bisa fashin bakin da aka yi na wannan kididdiga ta nuna cewa, fannin da bai shafi man fetir ba; shi ne kan gaba wajen ciyar da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasar gaba tare da samar da bayanai kan amfanin gona, kasuwanci da kuma kayan da ake sarrafawa.
Fannin da bai shafi man fetir din kuma ba, ya samar da kashi 94.30 ga tattalin arzikin Nijeriya a zango na biyun 2024, wanda ya yi kasa da kashi 93.62 a 2023, hakan ya nuna cewa; ya kai kashi 94.66 sama da wanda aka samu a zango na farko a 2024, da ya kai kashi 93.62.
Shi ma a nasa jawabin, kwamishinan ma’aikatar noma da samar da wadacaccen abinci, Otunba Faseru na Jihar Osun ya sanar da cewa, dole ne Nijeriya ta karfafa mayar da hankali kan noma, domin samun riba.
“Muna da komai da za mu iya habaka fannin aikin noma a wannan kasa, domin kuwa Allah ya albarkace mu da wadatacciyar kasar noma mai kyau, ga shi kuma muna da ruwan da za mu iya yin noma da shi har sau biyu a shekara”.
A jawabinta na maraba, Manajan Darakta kuma babbar jami’a a bankin Zenith, Adaora Umeoji; ta sanar da muhimmancin da ke tattare da fannin da bai shafi harkokin man fetir ba, musamman wajen kara samar da ayyukan yi.