Gidauniyar Pink Africa, ta ce har yanzu adadin masu warkewa daga cutar kansar mama a Nijeriya, ya yi kaɗan sakamakon rashin gano ta da wuri da kuma rashin fahimtar da jama’a game da cutar.
Babban Daraktan Gidauniyar Victor Ekpo, ne ya bayyana haka a garin Calabar, yayin wani taron wayar da kan jama’a da suka shirya haɗin gwuiwa da cibiyar kula da cutar daji ta Asi Ukpo da ƙungiyar mata likitoci ta Nijeriya (MWAN), da sauran ƙungiyoyi don wayar da kan jama’a game da cutar.
- Neman Haifar Da Baraka A Yankin Taiwan Jigo Ne Na Illata Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Gabar Tekun Taiwan
- WHO Za Ta Kwashe Mata Da Kananan Yaran Gaza 1,000, Zuwa Turai Don Kula Da Lafiyarsu
An keɓe watan Oktoba da masa laƙabi da “Pink Month” don wayar da kan jama’a game da cutar sankarar mama da yadda gano ta da wuri zai taimaka wajen ceton rayuka, inda daraktan ya ce suna gudanar da bikin a ƙasashen Afrika da dama da nufin kawo ƙarshen cutar daji.
Da take magana, shugabar ƙungiyar ta MWAN, a Cross Rivers, Dr. Minika Hogan-Okon, ta ce ana iya warkewa daga ciwon mama idan an gano shi da wuri amma likitoci ba za su iya magance ta ba idan aka makara, inda ta nuna damuwa kan matsalar ƙarancin cibiyoyin ciwon daji cikin al’umma da kuma tsadar magani da ya fi ƙarfin talaka.
Kwamishiniyar harkokin mata a jihar Edema Irom, ta ce wannan tattaki ba kawai zai tsaya a iya gangami ba ne, za a ci gaba da faɗakarwa da kuma wayar da kai, tare da tabbatar da cewa za su sanar da sauran jama’ar yankunan karkara.