Farfesa Humphrey Nwosu, tsohon Shugaban hukumar Zaɓe ta ƙasa (NEC), ya rasu yana da shekaru 83.
An haifi Nwosu ranar 2 ga Oktoba, 1941, kuma ya rasu a wani asibiti da ke Virginia, Amurka. Nwosu ya jagoranci NEC daga 1989 zuwa 1993, wadda yanzu ake kira hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC).
- Laifukan Zabe Barazana Ne Ga Samun Sahihan Zabuka A Nijeriya – INEC
- Mutum 2,629,025 Ke Da WuÆ™a Da Namar Zabo Sabon Gwamnan Edo -INECÂ
An naɗa shi ne lokacin mulkin Soja na Janar Ibrahim Babangida, kuma ya shahara bayan jagorantar zaɓen tarihin ranar 12 ga Yuni, 1993, wanda aka yabawa a matsayin mafi inganci a tarihin Nijeriya.
A wannan zaÉ“en ne É—an takarar SDP, Moshood Abiola, ya samu rinjaye kan Bashir Tofa na jam’iyyar NRC. Nwosu ya gabatar da sabbin tsare-tsare kamar Option A4 da tsarin buÉ—aÉ—É—en zaÉ“e.
Duk da ƙoƙarinsa na bayyana sakamakon zaɓen, Babangida ya dakatar da ci gaba da bayyana sakamakon.
A watan Yuli na 2024, majalisar wakilai ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya girmama Nwosu saboda rawar da ya taka wajen zaɓen ranar 12 ga Yuni.