A wani sabon hukunci, Babbar Kotun Jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) da ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben ƙananan hukumomin da aka shirya yi ranar Asabar, 26 ga Oktoba.
Wannan hukuncin ya saɓa wa na wata babbar kotun tarayya a Kano, wadda ta soke sahihancin kafuwar hukumar zaben.
- Sarki Sanusi II Zai Naɗa Babban Ɗansa A Matsayin Ciroman Kano
- NSCDC Ta Cafke Hatsabibin Ɗan Bindiga A Kano
Mai Shari’a Sanusi Ma’aji, wanda ya jagoranci shari’ar da KANSIEC ta shigar kan jam’iyyar APC da wasu, ya tabbatar da cewa KANSIEC na da cikakken iko na kundin tsarin mulki wajen gudanar da zabe a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Hakazalika, ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da kare lafiyar masu kaɗa ƙuri’a tare da kiyaye doka a ranar zaben.
Tun a farkon makon nan, mai Shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya ya dakatar da zaɓen bisa zargin cewa shugaban KANSIEC na da alaƙa da jam’iyyar NNPP mai mulki.
Wannan hukunci ya janyo cece-kuce tsakanin jami’an gwamnati da ƙungiyoyin farar hula, waɗanda suka bayyana damuwarsu cewa hakan na barazana ga ‘yancin dimokuraɗiyya a Kano.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi watsi da umarnin kotun tarayyar, yana mai tabbatar da cewa zaɓen zai gudana kamar yadda aka tsara.