Jami’an rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya Abuja sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne bayan wani kazamin fada da suka yi da ‘yan bindiga.
Wasu gungun masu garkuwa da mutane sun kai farmaki wani gida a unguwar Kubwa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja da sanyin safiya bayan da suka gamu da ‘yansanda, inda suka bude wuta tare da gudu zuwa wata fadama da ke kusa.
- Gwamnatin Tarayya Da Google Sun Bullo Da Hanyar Samar Wa Da Matasa 2,500 Aikin Dogaro Da Kai
- Tsohon Shugaban INEC, Farfesa Humphrey Nwosu Ya Rasu
Wakilinmu ya ruwaito cewa ‘yansandan sun bi sawun barayin, inda suka kama daya daga cikinsu tare da kwato wata motar gungun barayin.
Da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, Tunji Disu, ya tabbatar da cewa an kama daya daga cikin masu garkuwa da mutanen tare da kwace makamin dake hannunsa.
Ya ce ‘yan sandan sun yi gaggawar kai dauki ne saboda kiran da daya daga cikin mazauna yankin ya yi.
Disu ya bukaci mazauna yankin da su gaggauta tuntubar layukan gaggawa na rundunar a duk lokacin da suka ga abubuwan da ba su dace ba a muhallinsu.
Ya ce, “An yi sa’a an kama daya daga cikinsu, wasu kuma sun tsere. Sannan kuma mun kwato musu bindiga kirar AK-47 da harsashi mai rai guda 20, da bindigar Beretta da harsashi 12 a cikinta.
“Muna kokarin kama wasu da suka tsere. Yana da mahimmanci a lura cewa muna so mu gode wa wadanda suka ga lamarin kuma suka kira ‘yan sanda da sauri.
Muna rokon jama’a kada su tsaya jira yayin da suka ga wani da zai kawo rashin zaman lafiya ba tare da daukar mataki ba. Su yi la’akari da duk wani mataki da ke faruwa, da zarar sun ga wani yanayi da ya yi kama da fashi, su kira shashen gaggawa ‘yan sanda za su kawo daukin gaggawa.
“Don haka ina so in gode wa wanda ya kira mu mu dauki matakin gaggawa. Zan yi iyakacin kokarina domin nemo wadanda da suka tsere daga wurin da lamarin ya faru don neman mafaka. “