Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya nuna cikakken tabbaci kan nasarar jam’iyyar a zaɓen gwamna da za a gudanar a Jihar Ondo a ranar 16 ga Nuwamba.
Da yake jawabi a Akure yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan Ondo na Jam’iyyar APC, Ganduje ya bayyana cewa za a gudanar da zaɓen cikin gaskiya, kuma ya yi fatan jam’iyyar za ta samu rinjaye mai yawa.
- Zaben Kananan Hukumomi Ya Bar Baya Da Kura A Wasu Jihohi
- NNPP Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi A Kano
Ya buƙaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaben guda 305, ƙarƙashin jagorancin gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, su haɗa kai da sauran mambobin a matakin jiha don tabbatar da nasara.
A jawabinsa na karɓar jagoranci, gwamna Sanwo-Olu ya tabbatar wa shugabannin APC cewa kwamitin zai yi aiki tuƙuru domin samun nasarar da rinjaye mai yawa, yana fatan samun sama da kaso 80 na kuri’un zaɓen. Ya jaddada cewa za su gudanar da yaƙin neman zaɓen bisa ga manufofin nasara, suna goyon bayan nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa.