Arewa ce ta fi fama da matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki a Nijeriya, kamar yadda gwamnoni da sarakunan yankin suka bayyana a ranar Litinin 28 ga watan Oktoba.
Sun bayyana haka ne a yayin taron gaggawa na gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) da sarakunan gargajiya da aka yi a Gidan Gwamnatin Kaduna (Sir. Kashim Ibrahim House) don magance matsalolin da yankin ke fuskanta.
- Bangarorin Masana’antu Da Kasuwancin Kasar Sin Sun Bayyana Adawa Da Matakan Kariyar Ciniki Da Kasar Amurka Ta Dauka
- APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Gwamnan Ondo – Ganduje
Taron ya samu halartar Gwamnonin Arewa daban-daban da sarakunan gargajiya karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa.
Da yake jawabi a yayin taron, shugaban kungiyar kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce a matsayinsu na shugabannin Arewa, dole ne Gwamnonin su dauki matakan rage radadin talauci da mafi yawancin mazauna yankin ke fama da shi ta hanyar wanzar da shirye-shiryen walwalar jama’a, tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu da kuma nemo masu saka hannun jari zuwa yankin.
Ya yi kira da a samar da cikakken garambawul a dukkanin cibiyoyi, yana mai cewa, a halin yanzu suna ci gaba da yin kwaskwarima a manufofi da tsare-tsaren NSGF domin karfafa ayyukan kungiyar, wanda zai ba ta damar magance kalubalen da ake fuskanta yadda ya kamata.
Kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta magance matsalar wutar lantarki da ke addabar yawancin Jihohin Arewa sakamakon lalata turakun layin wutar lantarki da bata-gari suka yi.
Kungiyar ta amince cewa, Arewacin Nijeriya yana da dimbin albarkatun noma, wanda idan aka yi amfani da shi yadda yakamata, zai rage yunwa da bunkasar tattalin arziki. Don cimma wannan buri, kungiyar ta kuduri aniyar bayar da tallafin da ya dace ga manoma, da suka hada da samar da kudade, dabarun noman zamani da ababen more rayuwa kamar tituna da samar da ruwa don noman rani. Ba wai kawai a kalli noma a matsayin hanyar ciyar da al’ummarmu ba, har ma a matsayin hanyar samar da masana’antu da samar da ayyukan yi a fadin yankin. Za a iya cimma hakan ta hanyar sake farfado da masana’antun tufafi a Arewa
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce, yankin bai rasa wani rahoto ko mafita ba kan kalubalen da yake fuskanta, sai dai rashin aiwatar da shawarwarin da aka bayar kan magance kalubalen da aka gano.
Sarkin Musulmi ya umarci shugabannin yankin da su marawa shirin gwamnatin tarayya baya na magance matsalar Almajirci da yaran da ba sa zuwa makaranta.
Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, wanda ya yi jawabi a wurin taron NSGF, ya ce dakarun sojin suna aiki tukuru domin magance matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin Arewa da ma sauran sassan kasar nan.
Musa ya yabawa gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya bisa goyon baya da hadin kai da suke bayarwa don magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa.
A karshe, kungiyar NSGF ta yabawa mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da babban kwamandan rundunar sojojin tarayyar Nijeriya, Janar Christopher Musa bisa shirin kawo sauyi a bangaren kiwon dabbobi tare da amincewa da bayar da duk wani abu da ake bukata wajen tabbatar da nasarar gwamnatin tarayya wajen shirin bunkasa kiwon.